Ƴan Sanda A Gombe Sun Kama Mutane 23 Bisa Zargin Aikata Laifuka Daban-daban

0
44

Ƴan Sanda A Gombe Sun Kama Mutane 23 Bisa Zargin Aikata Laifuka Daban-daba

Daga Yunusa Isa, Gombe

Rundunar Ƴan Sandan Najeriya Reshen Jihar Gombe ta kama wassu mutane 23 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban da suka haɗa da haɗin baki, fashi da makami, sata da karɓar kayan sata, fyaɗe, sojan gona, kisan kai, mallakar tabar wiwi da miyagun kwayoyi.

Da yake gabatar da waɗanda ake zargin a madadin kwamishinan ‘yan sandan jihar CP Hayatu Usman, Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ASP Mahid Muazu Abubakar, yace an kama waɗanda ake zargin ne a lokuta daban-daban yayin samamen yau da kullum dana musamman da jami’an rundunar suka kai.

Mai magana da yawun ‘yan sandan yace an kama mutanen 23 da ake zargin ne da laifuka 9, inda aka yi nasarar kwato abubuwan da suka haɗa: Babura ƙirar Bajaj guda uku, da babbar mota tirela, da ƙunshin ganyen wiwi 88 da fakitin miyagun kwayoyi 110 da wayoyin hannu, da akwatunan talabijin, da gatari, da katin shaidar ɗan sanda na bogi da fular sojoji da dai sauransu.

Mahid Muazu yace rundunar ba za ta yi wata-wata ba wajen daƙile masu aikata laifuka a lunguna da saƙo na jihar.

Ya kuma yi ƙira ga al’ummar jihar su tallafawa jami’an tsaro da muhimman bayanai don daƙile ɓata gari tun daga tushe.

Ya ƙara da cewa da zarar an kammala bincike za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu don su fuskanci shari’a.

 

Hafsat Ibrahim