Efik: Tarihi, aure, abinci, da adini na wannan kyakkyawar ƙabilar

0
300

 

Yana da mahimmanci a bayyana anan cewa ban da mahaifarsu ta yanzu, mutanen Efik sun mamaye kudu maso yammacin Kamaru ciki har da Bakassi.

 Ya ɗauki mutanen Efik sama da shekaru ɗari biyar na yin ƙaura don zama a yankin gabar teku na Kudu maso Gabashin Najeriya, Jihar Cross River a karshe.

 Kodayake ba a san ainihin asalin mutanen Efik ba amma tatsuniyoyin gargajiya sun nuna cewa sun yi baƙunci daga Nubia har izuwa Ghana sannan Arochukwu a Kudu maso Gabashin Najeriya.

Ba a bayyana tsawon lokacin da hijirarsu ta kai su zuwa Arochukwu ba, amma abin da aka sani shi ne Efiks sun zauna cikin kwanciyar hankali a matsayin baki na kimanin shekaru dari hudu watto daga karni ta 11th – 15th tare da Aros.

Daga basanni suka tafi bayan rashin jituwa ta shiga tsakanin su da mai masaukin su.

A lokacin kashi na biyu na hijirar su wanda ya sa suka bar Arochukwu, mafi yawan su sun tafi Uruan a jihar Akwa Ibom ta yanzu, yayin da wasu kalilan suka tafi Eniong da yankunan da ke kusa da shi.

Kuma kamar yadda kakanninsu suka yi a Arochukwu, sun zauna lafiya a Uruan.

Ko dayake,  sun sake ƙaura daga Uruan ba tare da tarihi ya gaya mana dalilin da ya sa ba. Kuma lokacin da suka yi hijirar, sun sami kansu cikin Ikpa Ene da Ndodihi.

Amma a wannan karon, ɗan gajeren zama ne da suka yi kafin su tsallaka zuwa makomarsu ta ƙarshe a Garin Creek (Esit Edik / Obio Oko).

Garin Creek da kewayenta shine abin da ake kira Calabar a yau.

Har izuwa shekara ta 1954 kafin ta sami ‘yancin cin gashin kai, wannan yanki tsohon yanki ne na amana daga Jamhuriyar Kamaru wanda aka gudanar a matsayin wani yanki na Yankin Gabashin Najeriya.

Sai bayan cin gashin kansu ne rabe -raben siyasa ya faru.

Gaba ɗaya, tarihin hijirar Efik da ƙauyuka da mazauna yana da matakai guda uku a jere; (a) lokacin Ibo (b) matakin Ibibio da (c) guguwar zuwa bakin teku.

Kuma saboda wannan dalilin ne yanzu Efiks ke da alaƙa da Annang, Ibibio, Igbo, Oron, Biase, Akampkpa, Uruan, da Eket.

Al’adar aure a kabilar efik

Tsohuwar al’adar ‘Dakin Kiba’ watto fattening room a turance shine abu na farko da ke zuwa zuciya a duk lokacin da za a tattauna wannan batun (auren a kabilar Efik).

Kodayake an inganta shi sosai a wannan zamanin na yau, al’adar ɗakin kiba  na mutanen Efik shine keɓaɓɓen horo da ake baiwa kuyangi don shiryasu zama mace.

Watanni shida kafin yin aure, ana tura ‘yan matan Efik zuwa ɗakin kiwo don a yi musu ado da tausa daga kai har zuwa yatsa; ciyar da su gwargwadon yadda suke so su ci, da kuma ilmantar da su kan zamantakewan aure.

Ba’a  barin su, su yi wani aiki.

Maimakon haka za su ci abinci mai ɗimbin yawa, su yi taɗi mai ma’ana, su yi barci;  tare da yin masu tausa sau uku a kowani rana waɗa yin haka zai taimaka wajan fitar masu da siffar jikin iya mace mai kyau .

 Domin mutanen Efik sunyi imanin cewa macen da siffar jikinta ya cika da lafiyayyen kugu tana da kyau.

Baya ga ayyukan matakin dakin kiba watto Fattening room wadda muka ambata a baya, yarinyar tana samun horo na cikin gida na kula da gida (kamar dafa abinci, kula da yara, da kula da gida) da yadda ake girmama mijin ta da iyalin sa.

Hakkin tsofaffin mata ne su ba da shawara game da ƙwarewar da suka samu a aure don tabbatar da nasara.

Har ila yau, a cikin horon akwai raye -raye na al’adu (Ekombi), almara, tatsuniyoyi, waƙoƙi da sauran nau’ikan nishaɗi. Hakanan ana koyar da dabarun zane -zane akan kwarya da sauran kaya.

A nan ne kuma ake koyar da ita game da jima’i da nufin ba wa mijinta isashen gamsuwa da ta dace.

A watanni shida na karshe, wanda kuma ya kawo ƙarshen kwanakin keɓewa, ana gayyatar mutane ko’ina don girmama nasarar da ta samu ta wuce wannan mawuyacin halin.

Ana yin wannan bikin tare da raye -raye na gargajiya na Efik (Ekombi) da sauran nau’ikan nishaɗi.

Ana ci gaba da gudanar da bikin a duk tsawon yini da dare yayin da iyalai, abokai da masu kyakkyawar fata ke bayyana farin cikinsu da farin ciki tare da kyaututtuka da gudummawa ga amarya.

Kuma a ƙarshe, ita da mijinta na za su rungume juna suna rawa; yayyin da suke maraba da masu yin masu fatan alheri da suka zo taya su murnan bikin.

Abincin gargajiya na Efik

Sakamakon abubuwan da ke nuna rarrabuwarsu, abincin Efik galibi waɗanda aka samo daga koguna ne.

 Duk dangin Efik da ƙabilar su basa rabuwa da kogi ko rafi. Kuma saboda wannan, al’adun abinci mai gina jiki su ma yana da alaƙa da tekuna.

Dangane da al’adar Efik, ana ɗaukar Abassi a matsayin Babban Mahalicci. Kuma an san matarsa, Atai, a matsayin mai sasantawa.

An kuma yi imanin cewa Atai ce ta shawo kan Abassi ya kyale mutane biyu (namiji daya da mace daya), wanda kuma aka ce yayansu ne, su rayu a Duniya, amma ya hana su aiki ko haihuwa.

 

An bukaci yaran su koma sama tare da Abassi a duk lokacin da ya buga kararrawar abincin dare. An kafa waɗannan ƙa’idodin don kada mutanen Efik su wuce Abassi cikin hikima ko ƙarfi.

 

Amma kamar labarin annabiAdam na Littafi bible, yara sun yi rashin biyayya kuma Abassi bai kashe su kawai ba, Ya kuma la’ance su da hargitsi da mutuwa.

 

 

By: Firdausi Musa Dantsoho