Gwamnan Gombe Ya Jaddada Ƙudurinsa Na Inganta Walwala Da Jin Daɗin Ma’aikata, Tare Da Alkawarin Bada Fifiko Ga Tsaro Da lafiyarsu

0
15

Gwamnan Gombe Ya Jaddada Ƙudurinsa Na Inganta Walwala Da Jin Daɗin Ma’aikata, Tare Da Alkawarin Bada Fifiko Ga Tsaro Da lafiyars

Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya CON, ya jaddada ƙudurinsa na inganta walwala da jin daɗin ma’aikata a Jihar Gombe, yana mai jaddada cewa gwamnatinsa ta fahimci muhimmancin samar da wadataccen albashi ga ma’aikata.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnan ya jaddada ƙudurin gwamnatinsa na tabbatar da ganin ma’aikata sun samu wadataccen albashi, yana mai yabawa ƙwarin guiwa da jajircewarsu wajen marawa ƙoƙarinsa baya wajen samar da makoma mai kyau ga Jihar Gombe.

A saƙonsa na fatan alheri ga jajirtattun ma’aikatan albarkacin zagayowar ranar ma’aikata ta duniya ta bana, Gwamnan ya yaba da gagarumar gudunmawar da kungiyoyin ƙwadago da ma’aikata baki ɗaya ke bayarwa a matsayin abokan hulɗa masu muhimmanci wajen ci gaban jihar.

Yace taken bikin na bana, “Tabbatar da Lafiya da Tsaron Ma’aikata a Kowane Yanayi,” ya dace da ƙoƙarin gwamnatinsa na kyautata jin daɗi da walwalar ma’aikata.

Gwamnan ya bayyana alfaharinsa game da nasarorin da aka samu ta wannan fanni, ya kuma yi alkawarin ci gaba da ɓullo da sauye-sauyen da za su kare lafiyar kowane ma’aikaci.

Ya jaddada ƙudurinsa na samar da ingantaccen yanayin aiki da kyautata hulɗa da ma’aikata da nufin bunƙasa ayyukansu da nausa shugabanci na nagari gaba.

Ya bayyana matuƙar godiya ga ƙungiyoyin ƙwadago bisa haɗin kai da goyon bayan da suke baiwa gwamnati, yana mai jaddada cewa goyon bayan da suke bayarwa ya taimaka matuƙa wajen samar da gagarumar nasara a Jihar Gombe.

Gwamnan ya bada tabbacin cewa jin daɗin ma’aikata shi ne babban abin da ya sa a gaba, yana mai nuni da yadda gwamnatinsa ke biyan albashi da kuɗaɗen fansho a kan kari da kuma ƙoƙarin da ake yi na biyan bashin da aka gada na kuɗaɗen gratuti ga tsofin ma’aikatan da suka yi ritaya a matakin jiha da ƙananan hukumomi.

Duk da ƙalubalen tattalin arziƙi da zamantakewa da ake fama da shi, gwamnan ya yi ƙiran sadaukarwa da haɗin kai don shawo kan su, tare da jaddada muhimmiyar rawar da ma’aikata ke takawa wajen haɓaka masana’antu, sauƙaƙa kasuwanci, da bunƙasa muhimman sassa kamar noma da sauran ababen more rayuwa.

Ya buƙaci ma’aikatan su ci gaba da nuna himma da jajircewarsu wajen gudanar da ayyuka, yana mai basu tabbacin cewa gwamnatinsa ta ƙuduri aniyar ci gaba da biyan buƙatunsu a kowane lokaci gwargwadon iko.

Ismaila Uba Misilli
Babban Daraktan Yaɗa Labarun Gwamnan Jihar Gombe

 

 

 

 

Hafsat Ibrahim