Mataimakin Shugaban kasa da kungiyar Gwamnonin Arewa Maso Gabas a yau, wajen ƙaddamar da sabon gidan gwamnatin Jihar a Bauchi. 

0
15

Daga Yunusa Isah kumo

 

Gwamnan Gombe Ya bi Sahun Mataimakin Shugaban Ƙasa Da Sauran Gwamnonin Arewa Maso Gabas Wajen Ƙaddamar da Sabon Gidan Gwamnatin Jihar Bauchi

Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya CON, ya marawa Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima GCFR baya, tare da sauran Gwamnonin Arewa Maso Gabas a yau, wajen ƙaddamar da sabon gidan gwamnatin Jihar a Bauchi.

A yayin taron an kuma ƙaddamar da dandalin Rilwanu Sulaiman Adamu, da wassu sabin gine-gine a harabar gidan gwamnatin.

Taron ya samu halartar manyan jami’an gwamnati a matakin jihohi da tarayya, da sarakunan gargajiya; ciki har da Mai Martaba Sarkin Gombe Alhaji Dr Abubakar Shehu Abubakar na 3 da sauran manyan baƙi.

A cewar Gwamna Bala Mohammed na Jihar ta Bauchi, ana sa ran sabin gine-ginen za su inganta harkokin gwamnati da kuma zama wata alama ta ci gaba, da nagarta da gudanar da mulki da hadin kai a jihar dama jihohin Arewa maso Gabas.

 

Ismaila Uba Misilli

Babban Daraktan Yaɗa Labarun Gwamnan Jihar Gombe.

 

 

Hafsat Ibrahim