Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa, Inuwa Yahaya Ya Bada Shawarar Ɗaukan Wasu Dabaru Huɗu “4D” Don Magance Tabarbarewar Tsaro A Yankin

0
18

Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa, Inuwa Yahaya Ya Bada Shawarar Ɗaukan Wasu Dabaru Huɗu “4D” Don Magance Tabarbarewar Tsaro A Yanki

…Yayin Da Gamayyar Ƙungiyoyin Arewa Ta Shirya Taron Gaggawa A Abuja

Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa kuma Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana wassu sabin dabaru 4 na tinkarar ƙalubalen rashin tsaro da ake fama da shi a yankin a ƙoƙarin da ake yi na lalubo mafita mai ɗorewa ga matsalar da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa.

Gwamna Inuwa Yahaya ya bada shawarar ɗaukan dabarun ne a wani taron tattaunawa kan matsalar tsaro mai taken “Hanyoyin Magance Tabarbarewar Tsaro a Arewacin Najeriya” wanda Gamayyar Kungiyoyin Arewa (CNG) ta shirya jiya Laraba a Cibiyar taro ta Sojin Najeriya dake Abuja.

A cewar shugaban ƙungiyar gwamnonin na Arewa, dabarun huɗu sun ƙunshi ko wane fanni a ƙoƙarin magance matsalar tsaro, waɗanda ke maida hankali kan inganta harkokin ci gaba; da inganta dabarun tsaro; da shirya tarukan tattaunawa; da kuma ƙarfafa hanyoyin diflomasiyya.

Yace makasudin hakan shine a samar da ingantacciyar dabarar da za ta magance ƙalubalen tsaro a yankin don tabbatar da ɗaukar matakai masu inganci da ɗorewa, sabanin matakan da ake ɗauka a baya, musamman don magance matsalar sace-sacen mutane don neman kuɗin fansa, da matsalar yan bindiga, da rikicin ƙabilanci dana addini da kuma rikicin manoma da makiyaya da dai sauransu.

“Don samar da hanyoyi daban-daban na tinkarar ƙalubalen tsaron da muke fuskanta, ina ba da shawarar yin amfani da wannan tsarin dana ƙira 4D, wato: Ci gaba, Tsaro, Tattaunawa da kuma Diflomasiya.
Game da ci gaba, yau Arewacin Najeriya ya kasance kuran baya a al’amuran ci gaba. Hakan ya bada damar ƙyanƙyashe duk wassu lamura na ta’addanci da rashin tsaro. Don magance hakan, dole ne mu haɗa kai don kakkaɓe matsalolin dake haifar da rashin ci gaba a Arewa, waɗanda suka haɗa da fatara, da jahilci, da rashin aikin yi, da ƙaruwar al’umma barkatai da kuma gurbacewar muhalli.
Dole ne a mu maida hankali kan farfaɗo da ayyukan more rayuwa, da inganta rayuwar al’umma, da noma, da samar da makamashin da ake iya sabuntawa, da ƙarfafa tattalin arziƙin zamani da kuma farfaɗo da muhallinmu, “in ji shi.

“A fannin tsaro, akwai buƙatar mu maida hankali sosai kan fannin, dole ne mu ƙarfafa hukumominmu don su iya tinkara da magance barazanar tsaron dake kunno kai. Hakan yana buƙatar ɗaukar ƙarin ma’aikata, da horas da su da inganta yanayin aikinsu, da samar musu kayan aiki da bunƙasa dabarunsu, da inganta fasahar leƙen asiri, da farfaɗo da fannin shari’a, da kyautata jin daɗin ma’aikata, da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa a cikin gida.
Haka nan ma tattaunawa ya zama wajibi; dole mu ɗabbaƙa al’adar riƙon amana, mu hana masu ƙoƙarin raba kanmu samun damar cimma munanan manufofinsu kamar yadda Marigayi Sir Ahmadu Bello ya bayyana cikin hikima. “Mu mutane ne masu bambance-bambancen ƙabila, yare da addini, waɗanda suke dunƙule wuri guda don maslaha, buri da fahimta iri guda, abubuwan da suka haɗamu sun fi waɗanda suka raba mu.” Don haka dole ne mu haɗa kai da ƙungiyoyin fararen fula, da malaman addini, da sarakunan gargajiya, da dukkanin masu ruwa da tsaki don tattaunawa da fahimtar juna a tsakanin al’ummominmu daban-daban,” inji shi.

Gwamna Inuwa ya ci gaba da cewa, “A matsayinmu na shugabanni, dole ne mu ɗauki nauyi tare da haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen ganin bayan wannar mummunar dabi’a, mu kuma yi hakan cikin gaggawa don tabbatar da tsaron lafiyar al’ummarmu. Ƙalubale ne da ya shafi rayuwar al’ummarmu baki ɗaya, wannar matsala ba ta banbance ƙabila ko addini, ba ruwanta da (mai kuɗi ko talaka, mai muƙami ko mai bi, ba yaro ko tsoho da ya tsira daga illolinta. kuma a matsayinmu na ƙungiya, za mu ci gaba da bada himma wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiyan yankinmu.

Gwamnan ya kuma nuna rashin jin daɗinsa kan yadda ake riƙon sakainar kashi ga matsalar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi a Arewa, yana mai cewa shaye-shayen miyagun kwayoyi na haifar da babbar barazana ga tsaro domin yana taka rawa sosai wajen ruruta matsalar tsaro a yankin, inda ya buƙaci shugabannin yankin su baiwa matsalar kulawar data dace don magance ta.

Yace “Batun shaye-shayen miyagun kwayoyi, da rawar da yake takawa wajen haddasa rashin tsaro, abu ne da ba a baiwa kulawar data dace ba, babbar barazana ce ga rayuwar matasanmu da makomarsu, dole ne mu yaƙi wannar matsalar, mu tsamo matasanmu daga wannan ƙangin dama magance gararambar da suke yi a tituna, in ba haka ba kuwa zasu zame mana wani bam wadda lokaci kawai yake jira ya tashi, sakamakon matsalolin tattalin arziƙi da zamantakewar da al’ummarmu ta samu kanta a ciki, waɗanda illar su za su shafi zamantakewa da haɗin kanmu”.

A nasu jawabin Mataimakin Shugaban Ƙasa Sanata Kashim Shettima (wanda ya samu wakilci) da ministocin tsaro Badaru Abubakar da Muhammad Bello Matawalle, sun jaddada aniyar gwamnatin tarayya na ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiyar Najeriya, tare da tabbatar da cewa Gwamnatin da Shugaba Tinubu ke jagoranta zata ci gaba da bada fifiko kan tsaron Najeriya dana al’ummarta a duk sassan kasar.

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar na 3, da Farfesa Attahiru Jega da Dr. Audu Ogbeh, da sauran waɗanda suka yi jawabi, sun bayyana cewa dole ne shugabanni da masu ruwa da tsaki su maida hankali kan magance tushen matsalar rashin tsaro a yankin don samar da mafita mai ɗorewa ga matsalar rashin tsaron dake barazana ga ci gaban Arewa.

Taron ya samu halartar gwamnonin jihohin Arewa da wakilan gwamnatin tarayya da tsofin shugabannin Najeriya da shugabannin sojoji da sauran hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki da ƙungiyoyin fararen fula.

Ismaila Uba Misilli
Babban Daraktan Yaɗa Labarun Gwamnan Jihar Gombe

 

 

Hafsat Ibrahim