Wani banki ya Kori ma aikaciyar sa, bayan mare gurbinta da AI

0
16

Wata tsohuwar ma’aikaciyar banki mai shekaru 65, Kathryn Sullivan, ta rasa aikinta bayan shekaru 25 tana hidima a Commonwealth Bank of Australia (CBA). An sallame ta ne a watan Yuli 2025 tare da wasu abokan aikinta da ke sashen karɓar kira, sakamakon shirin bankin na amfani da na’urar fasahar wucin-gadi (AI) don maye gurbin ayyukan mutane.

Abin mamaki, chatbot ɗin da ya kwace mata aikin ita ce ta taimaka wajen horaswa. Sullivan ta shafe makonni tana shirya amsoshi da jagororin aiki don inganta bot ɗin, wanda daga ƙarshe shi ya sa aka ga an rage buƙatar ayyukan ma’aikata. Ta ce bata san cewa taimakon da take bayarwa zai dawo ya zama dalilin rasa aikinta ba

Sullivan ta bayyana takaicinta da cewa ma’aikatan da aka sallama ba su ji an mutunta su ba, saboda bankin ya yi watsi da su tsawon kwanaki kafin ya bayyana gaskiya. Duk da cewa daga baya CBA ta ba da haƙuri tare da ba da damar dawo da waɗanda aka sallama ko kuma su karɓi diyya, Sullivan ta ƙi komawa, tana mai cewa babu tabbas game da amincin matsayinsu.

Lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce a Ostiraliya, inda ƙungiyoyin kwadago suka nuna damuwa game da yadda fasahar AI ke ƙara maye gurbin mutane a wuraren aiki. Sullivan ma ta yi jawabi a wani taro a majalisar dokoki, inda ta nemi a samar da dokoki da tsare-tsare don kare ma’aikata daga rasa ayyukansu saboda ci gaban fasahar zamani.

Bankin ya bayyana cewa ya fahimci yadda lamarin ya girgiza ma’aikata, amma ya ce ci gaba da amfani da AI zai taimaka wajen inganta tsaro da yaki da damfara. Duk da haka, masana harkar kwadago sun yi gargadin cewa irin wannan sauyi zai iya zama barazana ga dubban ma’aikata idan babu kariya ta doka.

Hafsat Ibrahim