Jami’an hukumar babban birnin tarayya Abuja a ranar Talata sun rusa wata haramtacciyar kasuwa da aka fi sani da Kasuan-dere, wata maboyar ‘yan iska da masu sayar da muggan kwayoyi.
Da yake jawabi bayan rushewar, Daraktan Sashen Kula da Cigaban Babban Birnin Tarayya Abuja, Mukhtar Galadima ya ce kasuwar da ke kan titin Hassan Musa Katsina, kusa da Kpaduma II a Extension na Asokoro na zama barazana ga mazauna yankin da masu wucewa.
Ya kara da cewa an mayar da wurin wani yanki da ake gudanar da ayyukan ta’addanci duk da kokarin da Hukumar ta yi na tsaftace wurin.
Galadima ya ce ayyukan bata-gari a yankin na kuma yin illa ga kyawon muhalli baki daya, don haka bai kamata a ci gaba da yin hakan ba.
“Mun rusa wurin kusan sau uku amma ana ci gaba da samun matsala, a wannan karon muna yin shi a karo na karshe kuma dole ne ya tsaya, muna bukatar tsaftace wurin da kuma inganta yanayin muhalli.
“Har ila yau, yana daga cikin manufofin gwamnati mai ci na tsaftar gari, wannan yanki daya ne da muke fara atisayen, yankin na da alaka da matsalar tsaro, bayanan da muka samu sun nuna cewa akwai ‘yan bata-gari, dillalan miyagun kwayoyi da sauransu.
“Aikin zai taimaka mana wajen kawar da ‘yan iska da masu safarar miyagun kwayoyi da suka mamaye wurin”.
Sakataren taimakawa, umarni da kulawa da sa ido a FCTA,Peter Olumuji, ya kuma ce yankin ya zama abin damuwa ga mazauna yankin saboda munanan dabi’u da ake tafkawa.
“Bayan tsaftace muhalli, za mu sanya matakan da za a bi don tabbatar da cewa muna da maki a nan, zai taimaka wa mutane su wuce nan a kowane lokaci ba tare da fargabar kai hari ba, za a ci gaba da gudanar da atisayen.
“Tawagar hadakar na rundunar za ta kasance cikin shirin ko ta kwana domin tabbatar da cewa babu wani abu da ya shafi jama’a.”
Hakimin kauyen Kpaduma, Cif Bitrus Yakubu ya yabawa hukumar babban birnin tarayya Abuja da ta zo ta ceto su daga hannun ‘yan bindiga.
“Wajen ya shafe sama da shekaru ashirin a nan amma a yau ya koma don amfanin mu, mun yi matukar farin ciki a matsayinmu na al’umma saboda yadda aka share mazauna yankin mun samu kwanciyar hankali.” Inji shi.
Daga Fatima Abubakar.