Hukumar kula da farashin lantarki ta ƙasa (NERC) ce ta amince da ƙarin kuɗin saboda tashin farashin man fetur da kuma karyewar darajar Naira.
Sai dai shugaban na NLC ya buƙaci gwamnati ta hana wannan ƙarin kuɗin wutar.
A cewarsa “dole ne ayi la’akari da adadin wutar da kamfanonin rarraba wutar lantarki ke kawowa da kuma ƙarfin aljihun masu amfani da lantarki wurin biyan kuɗin”.
Acikin sanarwar da kwamared Ajaaero ya fitar a Abuja, ya ce shirin na nuna halin ko in kula da halin da talakawar Najeriya ke ciki.
Yayi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta duba lamarin da kuma kawo maslaha.
Daga Fatima Abubakar.