Babban Hafsan Hafsoshin Tsaro (CDS), Janar Christopher Gwabin Musa, ya yaba wa Majalisar Dokoki ta kasa bisa gaggauta tantance Mukaddashin Hafsan Sojin kasa, Laftanar Janar OO Oluyede.
Janar Musa wanda ya shaida yadda aka gudanar da tantancewar a majalisun biyu, ya ji dadin yadda majalisar dattawa da kwamitocin majalisar dattawa suka tantance mukaddashin hafsan sojin.
Sanarwan da ke dauke da sa hannun Daraktan labarai na Tsaro da kwanan wata 27 ga watan Nuwamba Brigediya Janar Tukur Gusau, ya ci Gaba da Cewa,Janar Musa ya tabbatar wa Majalisar Dokoki ta kasa cewa Laftanar Janar Oluyede zai kawo sabon karfin gwiwa da dimbin kwarewarsa wajen yaki da rashin tsaro a matsayin shi na babban hafsan sojin kasa.
Ya kuma yi alkawarin cewa Laftanar Janar Oluyede zai gina kan gadon marigayi babban hafsan soji, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja.
CDS ta bayyana matakin gaggawa na majalisar a matsayin kishin kasa kuma ya dace a wannan mawuyacin lokaci.
Hukumar ta CDS ta jaddada aniyar rundunar sojojin Nijeriya (AFN) na tabbatar da tsaron kasa. AFN ta ci gaba da kasancewa da aminci ga hukumar da aka kafa don aiwatar da ayyukanta na tsarin mulki.
Daga Fatima Abubakar