Shugaba Muhammad Buhari ya rubuto wasikar da ta ba Shugaban Riko na kasa na APC damar gudanar da babban taronta na kasa

0
58
  1. Shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya) ya umurci gwamnonin jam’iyyar All Progressives Congress da su baiwa shugaban kwamitin riko na kasa Mai Mala Buni damar gudanar da babban taron jam’iyyar na kasa.

Shugaban ya bayyana haka ne a cikin wata wasika da  ya aike wa shugaban kungiyar gwamnonin Progressives Forum kuma gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu, mai kwanan wata 16 ga Maris, 2022.

Da yake jaddada cewa dole ne a gudanar da babban taron a ranar 26 ga Maris, Buhari ya ce tsige Buni a matsayin shugaban CECC na iya haifar da kararraki da kuma bata dukkan ayyukan APC da hukumar zabe mai zaman kanta.

Wasikar Buhari ta zo ne a daidai lokacin da ake ta yada cece-ku-ce tsakanin Gwamna Buni na Jihar Yobe da takwaransa na Jihar Neja, Abubakar Bello.

Karanta cikakkiyar wasikar:

Kamar yadda ku ka sani, jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a halin yanzu tana fuskantar zazzafar cece-kuce da wasu abubuwa na rashin tabbas da a karshe ka iya sanya shakku kan matsayinta da kuma yin tasiri ga matsayi da yiwuwar babban taronta na kasa.

Saboda abubuwan da suka faru a baya-bayan nan, jam’iyyar APC na fuskantar shari’o’i da dama da ke gabanta a kotunan kasar nan.

 

Buhari, Bello da Buni

Bugu da kari, jam’iyyar ta nuna gazawarta wajen ci gaba da batun samar da sauyi a shugabancin kwamitinta na rikon kwarya (CECC), ta hanyar da ta kunshi, doka da mutunta wa’adin da aka kayyade da kuma bukatar baiwa hukumar zabe ta INEC. isasshiyar sanarwa na lokaci da wurin da za a gudanar da taron ta.

Ko shakka babu, wadannan rigingimu da rashin tabbas kamar yadda muka lissafo a sama, suna da matukar barazana ga jam’iyyar; kuma zai iya haifar da rashin sanin ayyukanta, zabuka da kuma yiwuwar soke duk wasu ayyukanta da INEC ta yi. Wannan yana iya a ƙarshe ma ya kai ga ruɗewa da rashin wanzuwarsa.