Rundunar yan sandan babban birnin tarayya Abuja, ta yanke shawarar sassauta dokan hana zirga-zirga .

0
117

Rundunar yan sandan babban birnin tarayya Abuja, ta ce mazauna garin Abuja za su iya gudanar da harkokin su na ranar zabe .
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa ga manema labarai , dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sanda Josephine Adeh.
Rundunar yan sandan ta yanke shawarar sassauta dokar hana zirga-zirga kamar yadda aka sanar tun farko na jidawalin zaben kananan hukumomin yankin da zai gudana a ranar 12 ga watan faburairu 2022.
Don haka jami’an suna ba da shawarar ga jama’a da su ci gaba da harkokin su na yau da kulum ba tare da tsangwama ko cin zarafi daga ko wane bangare ba.
Kwamishinan yan sandan Mr Sunday Babaji (PSC)yayin da yake bada tabbacin samar da tsauraran matakan tsaro, kafin zabe,lokacin zabe da kuma bayan zabe.
Kwamishinan ya bukaci jama’a da su fito da yawan su domin kada kuri’an yan takaran da suke so.
Yayi kira ga jama’an yankin, da su yi takatsantsan tare da kai rahoto ga yan sanda ta layukan gaggawa kamar haka-
08032663913
08061581938
07057337653
08028940883.

By Fatima Abubakar