Rugujewar shatale talen Gidan Gwamnati: Masana sun ce tsarin zai ruguje nan ba da dadewa ba – Abba Gida Gida

0
59

Gwamnan jihar KANO, Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida Gida ya bayyana cewa an rusa shatale talen gidan gwamnati a daren jiya domin amfanin jama’a.

A cewar wata sanarwa da babban sakataren yada labarai na gwamnan jihar, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya rabawa maneman labarai a ranar Laraba, kafin gudanar da atisayen, gwamnati ta tuntubi kwararrun Injiniya a bangarorin da suka dace wadanda suka tabbatar da cewa ginin shatale talen bai da inganci. kuma zai iya rugujewa tsakanin 2023 da 2024.

“Wannan shi ne saboda an yi ta ne da soson katifa da da yashi marasa inganci maimakon siminti.

“Haka zalika , ginin ya yi tsayi da yawa ba za a iya sanya shi a gaban gidan gwamnati ba saboda yana  toshe hanyoyin sa ido kan tsaro.

“Bugu da ƙari, yana haifar da ƙalubalen zirga-zirgar ababen hawa a kewayen yankin saboda girmansa, tare da toshe ra’ayin direbobin da ke shiga duk hanyoyin da ke da alaƙa da zagayawa.

“Gwamnati na son bayyana cewa ya zama dole a rushe tsarin don sake ginawa cikin gaggawa da kuma ragewa don tabbatar da ganin kofar shiga gidan gwamnati da amincin masu ababen hawa”.

Firdausi Musa Dantsoho