Shugaba Bola Tinubu ya rattaba hannu kan dokar kare bayanan Najeriya, 2023 ta zama doka.
Dokar Kare bayanai ta Najeriya, 2023 ta ba da tsarin doka don kare bayanan sirri da kuma aiwatar da kariyar bayanai a Najeriya.
Dokta Vincent Olatunji, Kwamishinan Hukumar Kula da Bayanai ta Najeriya (NDPB) ne ya bayyana haka a taron tabbatar da tsarin NDPD Strategic Roadmap and Action Plan (SRAP) a Abuja.
An aika da kudirin dokar zuwa majalisar dattawa da ta wakilai domin tantancewa da kuma amincewa da shi a ranar Talata 4 ga Afrilu 2023 ta wata wasika daga tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.
“Yanzu doka ce, sabuwar dokar da aka kafa ta hukumar kare bayanan Najeriya ta maye gurbin NDPB da tsohon shugaban kasa Buhari ya kafa a watan Fabrairun 2022.”
Kwamishina na kasa ne zai jagoranci hukumar da alhakin kula da sarrafa bayanan sirri. (NAN).
Firdausi Musa Dantsoho