CP Hayatu Usman Ya Buƙaci Haɗin Kan Gombawa Don Yaƙi Da Ɓata Gari

0
32

CP Hayatu Usman Ya Buƙaci Haɗin Kan Gombawa Don Yaƙi Da Ɓata Gari

Daga Yunusa Isa, Gombe

Sabon kwamishinan ‘yan sandan Jihar Gombe CP Hayatu Usman, ya yi ƙira ga al’ummar jihar su haɗa kai da rundunar ‘yan sanda don daƙile aikata laifuka da ɓata gari a cikin al’umma.

Kwamishinan ya yi wannan roƙo ne yayin taronsa na farko da manema labarai a hedkwatar rundunar yau Talata.

Kwamishinan yace “‘yan sanda kaɗai ba za su iya tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi a kowane lungu da saƙo na jihar nan ba, don haka akwai buƙatar al’ummah su haɗa kai da mu don magance aikata miyagun laifuka”.

Yace ƙofofinsa a buɗe suke ga kowane ɗan ƙasa, yana mai ƙarfafa al’ummar jihar su riƙa kai rahoton duk wani motsin da basu gamsu da shi ba zuwa gare shi ko ofishin ‘yan sanda mafi kusa, yana mai cewa “tsaro alhaki ne na kowa da kowa”.

CP Hayatu Usman ya kuma yi ƙiran samun haɗin kai da fahimtar juna tsakanin hukumomin tsaro a jihar, yana mai jaddada cewa idan suka haɗa kai, za su sauƙe nauyin dake kansu cikin sauƙi.

Da yake gargaɗin jami’ai da dakarun rundunar kan su guji karɓar cin hanci da rashawa da cin zarafi ko tsangwamar jama’a, sabon kwamishinan ƴan sandan ya jaddada cewa har yanzu beli kyauta ne a kowane ofishin ‘yan sanda, inda ya ƙirayi jama’a su kai rahoton duk wani jami’in ɗan sanda daya buƙaci kuɗi kafin bada beli.

Ya ƙara da cewa, rundunar tana ɗaukan sabbin matakai na tabbatar da cewa Jihar Gombe ta ci gaba da zama lafiya tare da kakkaɓe miyagun laifuka a cikinta.

Da yake yabawa Babban Sufetan ‘yan sanda bisa damar da ya ba shi, sabon kwamishinan ya yabawa gwamnatin Jihar Gombe bisa irin goyon bayan da haɗin kan da take baiwa ‘yan sanda wajen gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

Hakazalika ya yabawa sarakuna iyayen ƙasa, da shugabannin addini dana al’umma bisa goyon bayan da suke baiwa rundunar, yana mai ba da tabbacin ƙarfafa wannar kyakkyawar alaƙa da ɓangarorin.

Sabon kwamishinan ƴan sandan ya kuma yaba da goyon bayan da kafafen yaɗa labarai ke baiwa rundunar ta hanyar yayata ayyuka da nasarorin da take samu.