Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya, ya ƙaddamar da wani sabon rukuni na rabon tallafin kayan abinci karo na 17 ga marasa galihu 214,500, wadda za a yi a runfunan zaɓe 2,218 dake mazaɓu 114 na jihar.
Da yake jawabi yayin ƙaddamar da rabon a Filin Wasa na Pantami, gwamnan yace gwamnatinsa ta duƙufa wajen tallafawa al’ummar jihar musamman talakawa da marasa galihu.
“Wannan rabo ya nuna cewa sadaukarwar da muke yi wajen taimakawa al’ummarmu dake cikin mawuyacin hali wani dabi’a ne na wannar gwamnati, kama daga lokacin annobar corona zuwa cire tallafin man fetur a baya-bayan nan, mun ɗauki matakan ragewa al’ummah raɗaɗin halin da suke ciki”.
Ya buƙaci kwamitin rabon tallafin ya tabbatar da adalci a aikinsa, yana mai tabbatar da cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci cin hanci da rashawa ko wane nau’i ba.
“Burinmu shi ne mu samawa al’ummarmu damar dogaro da kansu ta fuskar samarwa kansu abinci, ba wai a ko da yaushe su yi ta jiran irin wannan tallafin da ba zai ɗore ba”.
Da yake kira ga al’ummar jihar su ci gaba da taimakawa juna, Gwamna Inuwa ya buƙacesu su yi wa Jihar Gombe addu’a da Najeriya baki ɗaya.
Tun da farko a nasa jawabin shugaban kwamitin rabon kayan abincin kuma mataimakin gwamnan jihar Dr Manassah Daniel Jatau wanda shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin tarayya Abubakar Inuwa Kari ya wakilta, yace gwamnatin jihar tana sane da irin matsalolin tattalin arziƙin da al’ummar jihar ke fuskanta musamman na ƙarancin abinci.
Yace an kafa ƙananan kwamitocin masu ruwa da tsaki a matakin gundumomi da ƙananan hukumomi, don tabbatar da rabon kayan abincin cikin sauƙi.
Ya yabawa al’ummar jihar bisa natsuwa da bin doka da oda da suka nuna, duk da ƙalubalen da ake fuskanta na matsin tattalin arziƙi.
A jawabinsa na godiya a madadin waɗanda suka ci gajiyar tallafin, Mai Martaba Sarkin Gombe Dr Abubakar Shehu Abubakar na 3 ya yabawa Gwamna Yahaya bisa yadda a kullum yake taimakon marasa galihu musamman a wannan lokaci na taɓarɓarewar tattalin arziƙi.
Ya yi ƙira ga sauran ‘yan siyasa da masu riƙe da muƙamai su yi koyi da wannan karimci na gwamna Inuwa.
Daga Inusa Isa