Mun kama matashin da ya kunnawa masallata wuta a cikin wani masallaci – Ƴan Sandan Kano

0
18

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta tabbatar da kama wani matashi da ake zargi da cinnawa wasu mutane Wuta, a lokacin da suke tsaka da Sallar Asubar yau Laraba, a cikin wani Masallaci a garin Larabawar Abasawa da ke ƙaramar hukumar Gezawa a Kano.

 

Kakakin rundunar ƴan sandan SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwar da ya aikowa Tozali TV a yau Laraba, ya ce bayan samun rahoton faruwar al’amarin ne Kwamishinan ƴan sandan Kano CP Muhammad Usaini Gumel, ya tura tawagar jami’an su inda suka kai ɗaukin gaggawa.

 

Matashin da ake zargin mai suna Shari’u Abubakar ɗan shekaru shekaru 38, ya ce shine ya siyo Fetur ya kunna wutar inda ya wurgata a cikin masallacin, lamarin da ya sa mutane da dama suka ƙone a sassan jikin su.

Aƙalla mutane 24 ne suka ƙone bayan da matashin ya kunna musu wutar a cikin masallacin, wanda tuni jami’an mu suka kai su asibitin Murtala Muhammad da ke Kano, inda suke ci gaba da samun kulawar likitoci, “in ji SP Kiyawa”.

 

Kiyawa, ya kuma ce daga binciken farko da suka fara matashin ya tabbatar da cewa shine ya sayo Mai a gidan Mai a cikin wata roba, yazo ya kunna wutar, biyo bayan wani rikicin gado da a tsakanin sa da wasu daga cikin mutanen yankin su, inda shima hannayen sa biyu suka ƙone.

 

 

 

Hafsat Ibrahim