Babban Daraktanta, Alhaji Abbas Idriss, ya bayyana a ranar Lahadi, 8 ga watan Janairu, 2023, a Abuja cewa ambaliyar ta kuma lalata gine-gine 131.
Ya ce wadanda abin ya shafa sun kai 20,376, wadanda ke yankin Bwari sun kai 2,058, yayin da mutane 2,279 suka shafa a karamar hukumar Abaji.
“Ambaliyan ya kuma yi sanadiyar raba mutane 2,972 da gidaje su inda gidaje 102 suka lalace, yayin da aka ceci rayuka 9,813.
“A karamar hukumar Bwari, gidaje 343 ne suka rasa matsugunansu, gidaje shida sun lalace, an kuma ceto rayuka 41. Ba a samu asarar rai sakamakon ambaliyar ba.
“A karamar hukumar Abaji, mutane 380 sun rasa matsugunansu, gidaje 23 sun lalace, an kuma ceto rayuka 272.
“A AMAC, mutane 6,876 ne ambaliyar ta fara shafa a hanyar Ebano Hudu ta kogin Damagaza, Efab Estate, Lokogoma, Apo Dutsen Expressway, Carters Court, Apo da Trademore Estate, Lugbe,” inji shi.
Idriss ya kara da cewa an samu hadurran hadurran tituna 15 amma an warware su tare da hadin gwiwar hukumomin da abin ya shafa.
Daga Fatima Abubakar.