An kashe ‘yan Sanda biyu,yayin da aka kai hari kan ayarin motocin Gwamna Mala Buni

0
71

Wasu da ake kyautata zaton mayaƙan Boko Haram ne sun ƙaddamar da harin kwanton ɓauna kan ayarin gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni a kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu, kuma sun kashe ƴan sanda biyu, sannan wasu da dama a cikinsu sun jikkata.

Da maraicin ranar Asabar ne maharan suka ƙaddamar da harin ga ayarin gwamnan yayin da yake kan hanyarsa ta komawa Damaturu daga Maiduguri a yankin arewa maso gabashin Najeriya, bayan ya halarci bikin yaye ɗalibai karo na 24 da jami’ar Maiduguri ta shirya.

Wani da ya kasance cikin tawagar gwamnan sannan ya ɓuƙaci a sakaya sunansa, ya shaida wa Rediyo Tarayya cewa maharan sun yi wa tawagar tasu kwanton ɓauna ne sannan suka fara harbin motocin babu ƙaƙautawa.

“A gaskiya mun tsallake rijiya da baya. Maharan sun hari motocinmu ne tsakanin Beni Shiekh zuwa Mainok, kimanin tazarar kilomita sittin daga birnin Damaturu, fadar gwamnatin jihar Yobe bayan mun taso daga wajen taron bikin yaye ɗalibai a jami’ar Maiduguri.”

Ya kara da cewa: “Amma magana ta gaskiya, sai bayan ƙarfe shida muka fito daga Maiduguri zuwa Damaturu”.

Gwamnan Yobe Mai Mala Buni
Gwamnan Yobe Mai Mala Buni bayan ya sami labarin harin

Hakazalika wani shaidar gani da ido ya ce, “Yayin wannan farmakin nan take ɗan sanda guda ɗaya ya gamu da ajalinsa, daga bisani kuma wani ɗan sandan shi ma ya mutu sakamakon mummunar raunin da ya samu na harbin bindiga yayin harin.”

Ya kuma ce, “Sai dai lokacin faruwar harin gwamna Mai Mala Buni baya tare damu, sun koma birnin Abuja domin halartan wani taro” a cewarsa.

Yayin zantawa da Rediyo Tarayya ta wayar salula jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Borno ASP Nahum Daso ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai yace har yanzu rundunar tasu ba ta fitar da sanarwar a hukumance ba.

Yankin arewa maso gabashin Najeriya ya kasance mai matuƙar haɗari ga al’umomin yankin saboda hare-haren da ƙungiyar Boko Haram ta shafe shekaru tana kai wa.

 

Daga Fatima Abubakar.