An tabbatar da mutuwar mutum daya,yayin da aka samu barkewar cutar diphtheria a Abuja.

0
58

An tabbatar da barkewar cutar diphtheria a Abuja, cutar diphtheria mai saurin kisa a ta yi sanadiyyar mutuwar wani yaro dan shekara hudu cikin takwas da aka samu da cutar

Daraktan sashen kula da lafiyar jama’a na babban birnin tarayya Abuja, Sadiq Abdulrahman, wanda ya sanar da hakan a ranar Litinin a taron manema labarai, ya ce bayanan da suka samu sun tabbatar da cewa an shigo da cutar ne daga makwabciyar jihar Neja.

Ya bayyana cewa makonni biyu da suka gabata, an sanar da ma’aikatar game da yiwuwar bullar cutar a Dei-Dei, inda aka samu rahoton bullar cutar guda takwas.

Abdulrahman ya kara da cewa, nan take sashen ya dauki matakin daukar matakin gaggawa, inda ta tattara samfurorin da za a yi gwaji a dakin gwaje-gwaje na kasa da ke Gaduwa da kuma cibiyar yaki da cututtuka ta Najeriya, inda ya ce sakamakon  da ya zo a ranar Juma’ar da ta gabata. ya nuna cewa daya ya fito tabbatacce daga cikin takwas.

Darakta ya yi bayanin cewa Sashen na hada kai da jihohin da ke makwabtaka da su don dakile yaduwar cutar daga jihohin da ke yaduwa ta hanyar sanya ido kan iyakoki kamar yadda ya shawarci mazauna yankin da su dauki tsaftar jikinsu da muhimmanci.

A nasa bangaren, Shugaban hukumar kula da lafiya matakin farko, Ishaq Vatsa ya ce cutar diphtheria na faruwa ne ta hanyar kwayoyin cuta wadanda alamomin sun hada da zazzabi, yoyon  hanci, wahalar numfashi kuma ana iya kamuwa da su ta hanyar atishawa, digon ruwa, tari da cudanya da gurbatattun mutane.

Vatsa ya shawarci mazauna yankin da su ziyarci wuraren samar da alluran rigakafi sama da 400 a fadin yankin domin samun rigakafin cutar.

 

Daga Fatima Abubakar. 3