An bukaci daukacin mambobin majalisar zartaswar tarayya (FEC) da ke neman mukamai a zaben shekara ta 2023 da su yi murabus kafin ranar Litinin, 16 ga Mayu, 2022.
Ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed ne ya sanar da haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai na fadar gwamnati sakamakon taron majalisar ministocin tarayya da Buhari ya jagoranta a zauren majalisar da ke fadar shugaban kasa a Babban birnin tarraiya Abuja.
Ya ce an baiwa ministoci ranar 16 ga Mayu, 2022, su yi murabus daga mukaman su.
Ya ce mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ne kawai a matsayin zababben jami’in da aka kebe.
Ministan ya ce ba shi da hurumin yin magana a kan makomar sauran masu rike da mukaman siyasa da su ma ke neman mukamai amma ba mambobin majalisar ministoci ba.
Tuni dai wasu daga cikin ‘yan majalisar ministocin kasar suka fara karbar fom din takararsu na neman tsayawa takarar shugaban kasa, Gwamna da na ‘yan majalisu a dandalin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.
Mambobin majalisar ministocin tarayya da suka karbi fom din samun tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC sun hada da ministan sufuri, Rotimi Amaechi; Niger Delta, Godswill Akpabio; Aiki da kwadago, Chris Ngige; Kimiyya da Fasaha, Ogbonnaya Onu, Karamin Ministan Ilimi, Emeka Nwajiuba; da kuma Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Timipre Sylva.
Karamar ministar ma’adinai da karafa Uche Ogar ta samu fom din takarar gwamna domin samun tikitin takarar gwamna a jam’iyyar APC a jihar Abia, yayin da ministar harkokin mata Paulline Tallen ta bayyana burinta na tsayawa takarar kujerar Sanata a jihar Filato.
Hakazalika, babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a, Abubakar Malami, ya bayyana cewa zai tsaya takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar Kebbi.
Daga:Firdausi Musa Dantsoho