Gwamna Inuwa Ya Cika Da Jimamin Rasuwar Mahaifiyar Lamiɗo Akko; Yayinda Ya Jagoranci Tawagar Gwamnati Zuwa Sallar Jana’izarta a Kumo 

0
16

Gwamna Inuwa Ya Cika Da Jimamin Rasuwar Mahaifiyar Lamiɗo Akko; Yayinda Ya Jagoranci Tawagar Gwamnati Zuwa Sallar Jana’izarta a Kumo

 

Daga Yunusa Isah kumo

Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya CON, Ya Jagoranci Tawagar Gwamnatin Jihar Gombe Zuwa Sallar Jana’izar mahaifiyar Mai Martaba Lamiɗo Akko, Hajiya Aishatu Muhammad Atiku (Hajiya Adda) wacce ta rasu jiya Asabar tana da shekaru 88 bayan doguwar rashin lafiya.

 

Hakan ya fito ne a wata sanarwar da Babban Daraktan Yaɗa Labarun Gwamnan Jihar Ismaila Uba Misilli ya miƙawa Mujallar Tozali.

 

Da yake miƙa ta’aziyyar a madadin gwamnati da al’ummar Jihar Gombe ga Lamiɗon na Akko da sauran iyalai a fadar mai martaban jim kaɗan bayan kammala sallar jana’izar, Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana rasuwar marigayiyar a matsayin babban rashi mai kaɗa zuciya.

“Bayan shekaru da dama data shafe tana yiwa al’ummah hidima, a yau, wata babbar jigo ga al’umma ta faɗi, duk da irin ƙaunar da muke yiwa marigayiyar, ya zama dole mu binne ta, saboda abin da koyarwar Musulunci ta tanadar kenan”.

A tsawon rayuwarta, ta taka muhimmiyar rawa a matsayinta na uwa, hakan ya bayyana ne ta yadda kake tafiyar da al’amuranka tun lokacin da ka hau kan karagar mulki a matsayin sarki, wanda hakan ya nuna irin tarbiyyar da ta yi maka da sauran ‘ya’yan data haifa,” inji Gwamnan.

“Yayinda muka yi mata jana’iza, muna addu’ar Allah ya gafarta mata kurakuranta, ya karɓi baƙuncinta, ya shigar da ita Jannatul-Firdaus. A madadin ni kaina, da gwamnati, da al’ummar Jihar Gombe, muna miƙa ta’aziyyarmu ga iyalanta musamman Mai Martaba Lamiɗo Akko, Alhaji Umar Muhammad Atiku. Allah ya baku ikon jure wannan babban rashi”.

A nashi jawabin, Mai Martaba Lamiɗon na Akko ya yabawa Gwamna Inuwa Yahaya da muƙarrabansa bisa yadda suka taya su alhini a wannan lokacin da suke cikin jimami.

Yace yadda Gwamna Inuwa Yahaya nan take ya bar duk ayyukansa cikin gaggawa saboda wannan babban rashi da ya faru a Masarautar Akko, ya nuna yadda yake da kishin jama’a da kyautata rayuwar al’umma, yana mai addu’ar Allah ya yi masa jagora a harkokinsa na shugabanci.

 

“A yau iyalanmu da ɗokacin Masarautar Akko da al’ummar Akko, muna matuƙar godiya ga mai girma gwamna da ya nuna mana ƙauna a wannan lokaci na baƙin ciki, muna kuma godiya da addu’o’in da kuka yiwa mahaifiyarmu da ta rasu, Allah ya saka muku da alheri. Kuma muna baka tabbacin cewa za mu ci gaba da ba da goyon baya, da yin addu’o’i don samun nasarori a dukkan ayyukan da kake yi a tsawon mulkinka,” in ji Sarkin.

Gwamna Inuwa Yahaya ya samu rakiyar Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Gombe Rt. Hon. Abubakar Muhammad Luggerewo, da Sakataren Gwamnatin Jihar Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi, da Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnati Alhaji Abubakar Inuwa Kari, da babban sakataren gwamna wato PPS da sauran manyan jami’an gwamnati da kuma jiga-jigan Jam’iyyar APC irinsu Alhaji Jamilu isiyaka Gwamna, da Hon. Ismaila Mu’azu Hassan da kuma Alhaji Abubakar Shareef.

 

 

 

Hafsat Ibrahim