25/12/2023
Gwamnan Gombe Ya Taya Murna Ga Kiristoci, Tare Da Jaddada Muhimmancin Zaman Lafiya, Ƙauna Da Nazari
…Ya Buƙaci Su Yi Wa Najeriya Addu’o’i
Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya CON, ya taya mabiya Addinin Kirista a faɗin jihar murnar zagayowar bikin Kirsimeti na bana.
A cikin saƙonsa na fatan alheri kan murnar zagayowar bikin na bana, Gwamna Inuwa Yahaya ya buƙaci mabiya Addinin na Kirista da ɗokacin al’ummar jihar, su rungumi darussan da Kirsimeti ke koyarwa a irin wannan lokaci, waɗanda suka ƙunshi ƙauna, zaman lafiya, sulhu, da zurfafa tunani.
Ya kuma buƙaci al’ummar Jihar Gombe su ci gaba da haɗa kai cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakaninsu don kyautatuwar al’ummah.
“Yayin da muke bukukuwan wannan muhimmin lokaci, mu rungumi haɗin kai, ƙauna, tausayi da bege, tare da yiwa juna fatan alheri kamar yadda Yesu Almasihu ya koyar.
Gwamnnan ya jaddada muhimmancin yin amfani da wannan lokaci wajen yin addu’o’i wa ƙasar nan don kyautatuwa da ci gabanta, musamman a wannan mawuyacin lokaci da ‘yan Nijeriya ke fuskantar ƙalubalen tattalin arziki da zamantakewa.
“A tsaka da waɗannan ƙalubale da muke fuskanta, ina ƙira ga ɗokacin al’ummar Jihar Gombe dama na faɗin Nijeriya, da kada mu sare ko mu yanke ƙauna, amma mu ci gaba da ƙarfafa fata da bege, kuma mu bi tafarkin hangen nesan dake ƙunshe cikin Ƙudurin Sabunta Fata na Shugaba Bola Ahmed Tinubu GCFR. Ina da yaƙinin, za mu gina ƙwaƙƙwarar ƙasa mai cike da arziƙi da wadata ga kowa.”
Gwamna Inuwa ya jaddada ƙudurin gwamnatinsa na ɗorawa kan kyawawan nasarorin data samu a sassa daban-daban, da kuma ciyar da jihar gaba don kaita tudun mun tsira.
Ismaila Uba Misilli
Babban Daraktan Yaɗa Labarun Gwamnan Jihar Gombe