Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana ranar Juma’a 7 ga wata da Litinin 10 ga wata a matsayin ranar hutun Ista.

0
13

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun Juma’a 7 da Litinin 10 ga Afrilu, 2023 a matsayin ranakun hutu domin bukukuwan Easter na bana.

Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola ne ya bayyana hakan a Abuja.

Aregbesola, a wata sanarwa dauke da sa hannun babban sakataren ma’aikatar, Shu’aib Begore, a yau ranar Laraba, ya bukaci mabiya addinin kirista da su yi koyi da kyawawan halaye na sadaukarwa, hadin kai, gafara, kyautatawa, soyayya, zaman lafiya da hakuri wadanda halaye ne da ayyukan Yesu Kiristi, kamar yadda ya nuna a hidimarsa a duniya.

Ministan ya yi kira ga Kiristoci da dukkan ‘yan Najeriya da su yi amfani da bikin Easter na bana wajen yin addu’o’in kawo karshen matsalolin tsaro a sassan kasar.

Aregbesola ya ce “Tsaro aikin kowa ne. Don haka ina kira ga ‘yan Najeriya da baki mazauna kasarmu da su nuna kishin kasa da kishin al’umma ta hanyar mara wa kokarin jami’an tsaro goyon baya wajen samar da zaman lafiya da tsaron rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa”.

Ministan ya tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya na yin duk abin da ya dace don tabbatar da mika mulki cikin lumana bayan an gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali.

Yayin da yake yi wa kiristoci na gida da na kasashen ketare fatan murnar zagayowar ranar Ista da kwanciyar hankali, ya kuma umurce su da su so makwabtansu ta hanyar kyautatawa da karamcin ruhi, tare da masu hannu da shuni, tare da raba kayansu ga marasa galihu da ke kewaye da su.

Aregbesola ya sake tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa al’ummar kasar na nan a kan turbar daukaka kuma ya bukaci kowa da kowa da su yi amfani da karfinsu na kirkire-kirkire domin samun ci gaba mai zuwa.

 

Daga Fatima Abubakar.