Hukumar tsaftace muhalli ta himmatu wurin ganin ta kawar da duk wani aiki na ababen hawa ba tare da ka’ida ba.

0
32

Hukumar kula da babban birnin tarayya Abuja,  ta sake jaddada aniyar ta na kara zage damtse wajen kame duk wata ababen hawa, da kame wadanda suka ki bin wasu ka’idoji.

Hakan ya faru ne yayin da ta kame motoci 24 da kekuna 7 bisa laifuka daban-daban daga sassa daban-daban na yankin, a karshen mako.

Shugabar aiyuka na hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta a Abuja (DRTS), Deborah Osho, wacce ta jagoranci tawagar jami’an runduna ta hadin gwiwa kan ayyukan tabbatar da tsaro, ta ce dukkan hukumomin da abin ya shafa sun kuduri aniyar karfafa kai hare-hare kan duk wani nau’i na tashin hankali a cikin birnin.

Osho ta bayyana cewa, tun da masu motocin haya da sauran ababen hawa suka ki bin ka’ida, rundunar jami’an tsaro, ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kama su da gurfanar da su gaban kuliya.

“Aikin dai  ya shafi tsaftace garin ne, An yi nasarar kawar da barasa a kasuwar Garki daga wuraren ajiye motoci na haramtacciyar hanya, wannan aikin ya fara ne daga Area 1 zuwa 3, da kuma gadar Apo. Yanzu za a fadada shi zuwa yankunan kasuwar Garki.

“Masu motocin da aka kama da laifuka daban-daban, za su fuskanci kotun tafi-da-gidanka, motocin da ba su dace ba, dole ne a gyara su, su ma alkalan kotun tafi da gidanka za su tantance tarar su, mun kama motoci kusan 24.  da kekuna 7.

Bangaren muhalli na ayyukan, mataimakin darakta mai sa ido da tabbatarwa na hukumar kiyaye muhalli ta Abuja (AEPB), Kaka Bello ya ce wuraren da aka kai farmakin, wuraren da ayyukan bil’adama ke ci gaba da haifar da munanan matsaloli.

Bello ya kara da cewa, yakin da jami’an tsaro ke yi da wadanda ba su dace ba, shi ne tabbatar da cewa Abuja ta ci gaba da zama birni abin alfahari.

Ya bayyana cewa ana bukatar tsaftace muhalli a kullum, yana mai nuni da cewa dan kadan ba zai yi tasiri ba.

A cewarsa, “Mun himmatu wajen kawar da duk wata matsala a cikin birnin, musamman ma wadanda ke da illa ga muhalli. Dole ne a rika tsaftace muhalli a kullum.”

 

Daga Fatima Abubakar.