Hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya – DSS ta ce ‘yan ta’adda na shirin kai hare-hare a wuraren ibada da wuraren wasannin yara a lokutan bukukuwan babbar salla a ƙasar.
Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a shafinta na Twitter, ta shawarci masu kula da wuraren da al’umma ke zuwa ciki har da kasuwanni da manyan kantuna, da su riƙa lura da kai-komon mutane.
Hukumar ta kuma yi kira ga jama’a da su kai rahoton duk wani abu da suke ganin ba su amince da shi ba, zuwa ga jami’an taro.
Ya ce a wani samamen haɗin gwiwa da jami’an hukumar suka kai tare da sauran jami’an tsaro, sun ƙwato abubuwan fashewa daga hannu wasu ‘yan ta’adda.
Mista Afunanya ya ce sun samu nasarar kama wani mai safarar makamai a lokacin wani samame a kan babbar hanyar Abuja zuwa Keffi.
Haka kuma sanarwar ta ce hukumar za ta ci gaba da aiki tare da sauran jami’an taro domin fatattakar ayyukan ‘yan ta’adda a fadin ƙasar
Daga Fatima Abubakar.