Hukumomin daban-daban sun sha alwashin daukan matakan da suka dace a yankin Trademore Estate da ambaliyar ruwan sama ya afku.

0
30

Kwanaki biyu bayan wata mummunar ambaliyar ruwa da ta rutsa da gidaje akalla 116 a gundumar Lugbe, An  ayyana yankin Trademore Estate a matsayin yankin bala’i , wanda ke bukatar daukar matakin gaggawa don magance wasu barna da asarar rayuka da dukiyoyi. .

Don hakan ana duban fito da wani shiri na kwashe mutane daga wadannan yankuna, ta yadda za su kare afkuwar asarar rayuka a yankin.

Da yake bayani yayin wani taron gaggawa jiya ab Abuja akan akan lamarin, Babban Sakatare na birnin Tarayya Abuja, Olusade Adesola, ya ce lamarin ambaliyar ruwa a Estate Trademore, na daga cikin batutuwan da aka duba a taron kwamitin tsaro na wata-wata na babban birnin tarayya Abuja, domin yin la’akari da kokarin da ya kamata a yi domin dakile barnar dukiya da asarar rayuka. daga ambaliya.

Adesola, wanda ya jagoranci manyan jami’an Gwamnati,shugabannin jami’an tsaro a wani rangadin tantancewa a yankin da lamarin ya shafa, ya ce sun yi mamakin yadda kwanaki biyu kacal da aukuwar ambaliyar, mutane sun koma wasu kadarorin.

Sai dai ya kara da cewa babban sakataren bunkasa Abuja, wanda ke shugabantar kwamitin yaki da ambaliyar ruwa,Kwamishinan ‘yan sanda da sauran jami’a  musamman FEMA, Control Debelopment, AEPB a shirye suke su je su samar da hanyoyin da za su magance matsalar nan take.

Ya ce: “Mun ziyarci Trademore ne don ganin kalubalen ci gaban da ke tattare da yanayin magudanar ruwa da aka yi a kan titunan yankin, mun ga bukatar a duba lamarin cikin gaggawa.

“Mun yi matukar mamakin irin yadda ambaliyar ruwa ta afku a can (Trademore Estate) musamman irin hadarin da mutane suka yi – don yin gini a cikin wani fili mai tattare da hatsari ,Yayin da muke kan hanya, mun ga cewa hatta rufin gidaje  sun yi kasa da matakin titin, wanda hakan ya sanya su cikin hadari ga ambaliya.

“Rundunar da ke aiki nan take za ta zage damtse don ba da shawarwari kan batutuwan gaggawa ko kuma kulawa da ya kamata a bai wa yankin, saboda ba za mu iya nade hannayenmu ba mu bar barnar ta ci gaba.

“Mun yi mamakin cewa bayan kwana biyu kacal da aukuwar ambaliyar, mutane sun koma wasu kadarorin, don haka nan da kwanaki biyu za mu dauki matakin da ya dace, ganin yadda ambaliyar ta yi kamari, mun sanar da kaddarorin na Trademore Estate. yankin da ke fama da bala’i da ke buƙatar daukar matakin gaggawa don magance ƙarin barna da asarar rayuka da dukiyoyi.

“Don haka za mu duba wani shiri na kwashe mutane daga wadannan yankuna, domin tabbatar da cewa mun dakile asarar rayuka da dukiyoyi.

“A cikin sauran shekara, hasashen ruwan sama ya nuna cewa za a iya samun karin ruwan sama mai yawa, wanda ke nufin za a iya samun barna da asarar rayuka. Kuma za mu yi duk mai yiwuwa a cikin ikon mu don ganin mun dakile faruwar hakan.

Don haka ya bukaci mazauna yankin da su kasance masu kamun kai a wuraren da za su gudu, domin kada su shiga inda za su makale.

Daga Fatima Abubakar.