Shugaban kasa Bola Tinubu ya Gayyaci shugabannin kungiyoyin kwadagon Nigeria wadanda suka haɗar da NLC da TUC, a kokarin sa na dakile yajin aikin da suke shirin tsunduma a ranar talata wato 03 ga watan October.
Shugaban kasar dai yanzu haka yana ganawa da Shugabannin yan ƙwadago Wanda sanarwar ta ce “shugaban tun da misalin karfe 2 na ranar yau lahadi yana nemansu a fadar shugaban kasa dake Aso Rock Villa.
Idan za’a iya tunawa tun a makon da ya gabata kungiyoyin kwadagon suka bada sanarwar fara yajin aikin sai baba-ta-gani , sakamakon gazawar gwamnatin tarayya wajen cika alkawuran da ta dauka na shawo kan tarin matsalolin da yan Nigeria suke fuskanta tun bayan janye tallafin man fetur.
Daga Fatima Abubakar.