Mabarata 150 ne aka kora yayin da FCTA ta tsananta cunkoson bara a kan titunan babbar birnin tarayya.

0
192

Kimanin mabarata dari da hamsin (150) ne aka kwashe daga manyan titunan Abuja, babban birnin tarayya (FCT), bisa zarginsu da tayar da zaune tsaye da kuma kawo cikas ga zaman lafiya a birnin.

A karshen mako ne dai jami’an sakatariyar ci gaban jama’a (SDS) tare da hadin gwiwar hukumar kare muhalli ta Abuja (AEPB), Daraktan kula da zirga-zirgar ababen hawa, sashen tsaro na babban birnin tarayya da kuma ofishin babban mataimaki na musamman ga ministan babban birnin tarayya Abuja kan sa ido,dubawa da tabbatarwa ne suka gudanar da kwashe mabaratan da suka hada da mata da kananan yara  har da da tsoffi.

Hakan dai ya biyo bayan sabon matakin da FCTA ta dauka na dakile barace-barace a kan tituna a babban birnin  bayan korafe korafe da ake yi kan wannan barazana. An lura da cewa tawagar ta dauko mabaratan ne a titunan da ke da manyan kantuna,  masallatai da sauran wuraren barace-barace a cikin Maitama, Wuse II da Garki da sauran yankunan.

Sakatariyar cigaban jama’a (SDS), Hadiza Mohammed Kabir, wacce ta bayyana cewa FCTA na shirin kwashe mabarata tsakanin 400 zuwa 1,000 daga birnin, ta ce karamar ministar babban birnin tarayya ta fara kwashe mabarata daga tituna tare da tsaftace kewayen birnin. Abuja.

Ta kara da cewa zuwa lokacin da suka gama kwashe mabarata tare da yi musu sansani a wasu cibiyoyin FCTA, domin samun cikakkun bayanai, Ministan zaita tattauna da dukkan gwamnonin jihohinsu na asali, daga nan kuma za a mayar da su jihohinsu.

“Kamar yadda kuke gani a yau, Karamar Minista  Dr Rahmatu Tijjani Aliyu ta aika da gargadi mai karfi ta hannuna a matsayina na jagoran wannan tawaga zuwa gare su cewa su tashi daga kan tituna.

“Tuni ministan ta  aika musu da abinci da abin sha domin su ci su kuma yi buda baki da yamma, amma muna zuwa gare su idan ba su bar tituna ba, saboda su daina bara a titunan Abuja.

Sakatariyar ta kuma sanar da yin afuwa na minista da karamin ministan ya yi wa wadanda aka kora a karshen mako tare da gargadin cewa kada su koma bakin titi.

Hakazalika, babban mataimaki na musamman ga Ministan babban birnin tarayya Abuja, kan sa ido, dubawa da tabbatarwa, Ikharo Attah, ya ce abin da FCTA ta yi shi ne ta kwashe mabaratan daga tituna da kuma kai su wuri mai aminci, da kuma tabbatar da cewa sun samu kulawa na musamman.

Attah ya ce: “A cikin watan Ramadan da mafi yawan ‘yan uwa musulmi ke sadaukar da kansu wajen bautar Allah Madaukakin Sarki, mun ga barace-barace da suka wuce gona da iri wadanda daga sassan kasar nan ke kwararowa zuwa babban birnin tarayya Abuja, don yin bara.

Daga Fatima Abubakar