Rundunar ‘yan sanda ta kama wasu mutane 480 da ake zargi da hannu a aikata laifuka.

0
46

Rundunar hadin gwiwa ta jami’an tsaro ta hadin guiwa a babban birnin tarayya Abuja, a ranar Juma’a, ta kai samame a wasu gine-gine da ba a kammala gina su ba a unguwar Maitama da Wuse II a Abuja tare da cafke wasu mutane 480 da ake zargi da aikata laifuka.

Kwamandan da ke kula da tawagar, Bennett Igweh bayan kama su, ya ce an kama wadanda ake zargin ne biyo bayan namijin kokarin da rundunar ta keyi na yaki da aika miyagun laifuka.

Ya bayyana cewa wadanda ake zargin galibi maza ne da suka mayar da koren waje, wuraren da ba a gina su, gidajen da ba kowa a cikin su domin aikata laifuka.

Igweh ya ce tawagar ba za ta yi kasa a gwiwa ba  wajen yaki da masu aikata laifuka.

Ya bayyana cewa, kayayyakin da aka kwato daga hannunsu sun hada da kakin ‘yan sanda, wayoyin hannu, da bindigogi masu lodi, ashana da kuma laya.

A cewarsa, za a bayyana sunayen wadanda ake zargin su 480 tare da mika su ga hukumomin da suka dace domin daukar matakan da suka dace.

Igweh ya ce: “Mun kama mutane kusan 480 da ake zargi da aikata laifuka, za mu gurfanar da su a gaban kuliya.

“Kuma za mu yi cikakken bayanin saboda muna zargin cewa za a iya samun wadanda suka tsere daga gidan yarin Kuje.

“Za mu fara ne daga tsakiyar birnin, kuma za mu fadada shi zuwa wasu wurare, atisayen zai kai kauyuka da garuruwa 21 daga Kabusa, Gishiri, Waru, zuwa Wasa da sauransu, mun ce su,ko su nemi inda za su koma. ko kuma su sami matsuguni na halal da za su yi rayuwar su cikin doka da oda.

“Wannan farmakin da jami’an tsaro suka fara tun daga lokacin, mun kusa fara aikin G-7 amma muna so mu tsarkake tsakiyar birnin daga miyagu.

“Mun amince da yin hakan ne tare da  kwamandan wannan rundunar hadin gwiwa da ta hada da ‘yan sanda, Sojoji, Navy, Sojan Sama, Tsaron Najeriya da Civil Defence (NSCDC) , Hukumar Shige da Fice, DSS da sauran hukumomin ‘yan uwa. Kuma gaba dayan mu a hade, za ku ga sakamakon, mun fara da karfe 1:00 na safe yau har izuwa misalin karfe 3 na safe.

“Wadanda ake zargin sun kware wajen fashi da makami; suna da kakin jami’an tsaro daban-daban, mun kama su da kakin yan sanda.

“A daya daga cikin sansanonin mun kwato wata karamar bindiga cike da lodi saboda mun yi musu diran mikiya,shi ya sa muka samu nasarar kwato abin da muka kwato, za mu ci gaba da kai musu samamen ba zato ba tsammani, domin wannan aikin ba gudu babu ja da baya.

Daga Fatima Abubakar