Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya umurci Shugabancin APC da ta mayar wa duk wanda ya janye takara kudaden fom.

0
110

Shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), ya bukaci jam’iyyar All Progressives Congress da ta mayar da kudaden da ake amfani da su wajen siyan fom ga masu neman tsayawa takara da suka amince da yarjejeniya gabanin babban taron na ranar Asabar.

 Buhari ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ya yi da gwamnonin jam’iyyar APC a Abuja ranar Laraba, inda ya kara da cewa gwamnonin su tabbatar da cewa duk masu neman mukami a cikin kwamitin ayyuka na kasa sun fito ta hanyar bai daya.

 Daga nan ne shugaban ya baiwa gwamnonin sa’o’i 24 da su zayyana jerin sunayen wadanda za su tsaya takara a dukkan mukamai gabanin babban taron.

 Ya ci gaba da cewa, “Na riga na bayar da nawa shawara da sauran shawarwari kan yadda za a ci gaba a duk ganawar da na yi da shugaban kwamitin riko na ranar 25 ga Fabrairu, 2022 da wasikar da na rubuta a ranar 13 ga Maris, 2022 zuwa ga shugaban kungiyar gwamnonin APC. .

 “Masu daraja. Yayin da taron ya rage kwanaki biyu kacal, ina rokon ku da ku taru ku daidaita duk sauran mukaman jam’iyyar domin nan da sa’o’i 24 masu zuwa za mu isa jerin sunayen hadin kai da za mu kai zuwa babban taron.

 “Daga karshe duk wadanda suka sayi fom din da ke nuna sha’awa kuma aka sauke su a mayar musu da kudadensu ba tare da bata lokaci ba.”

 Buhari ya ce musamman gwamnonin da su sanya muradin jam’iyyar a gaba da nasu domin zai zama bala’i ga jam’iyyar PDP ta dawo mulki a 2023.

Fatima Abubakar.