Gwamna Inuwa Yahaya na jahar Gombe ya yi Allah wadai da kisar gillar da aka yi wa ,Sheikh Ibrahim Albani a gidan sa.

0
40

Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Yahaya, ya koka kan kisan wani malamin addinin Islama, Sheikh Ibrahim Albani, da wasu barayi suka yi wa kisan gilla a gidan sa da ke unguwar Tabra da ke wajen babban birnin jihar.

Yahaya wanda ya halarci sallar jana’izar marigayin a ranar Larabar da ta gabata a masallacin Bolari Izala da ke Gombe, ya yi Allah-wadai da kakkausar murya, wannan mummunan aika-aikar da ya ce ya girgiza al’amuran tsaro da kuma samar da zaman lafiya a jihar.

Ya ce, “Muna so mu tabbatar wa ‘yan jihar Gombe cewa gwamnati ta jajirce wajen kokarinta na tabbatar da tsaro da tsaron al’ummarta. Za mu ci gaba da daukar kwararan matakai tare da yin amfani da karfin da rundunar mu ke da shi wajen fatattakar masu aikata miyagun laifuka a kowane bangare na jihar, tare da gurfanar da wadanda ke da hannu wajen aikata wannan danyen aiki a gaban kuliya domin hana faruwar hakan.

“Kisar  Sheikh Ibrahim Albani ya  zama abin tunatarwa cewa dole ne mu kasance a faɗake da tsayin daka wajen neman al’ummar da kowa zai zauna lafiya ba tare da tsoro b

Ya kuma bukaci al’ummar jihar da su ci gaba da yin hadin gwiwa da juna, tare da hadin kai da malaman addini da suke wa’azi don fadakarwa.

Yahaya ya kara da cewa, “Jahar gaba daya ta yi alhinin rashin wannan malami kuma malami mai wa’azi da koyarwarsa da shiriyarsa suka taba rayuwar musulmi marasa adadi.”

Yahaya ya ce, “Marigayi Sheikh Ibrahim ya kasance mabubbugar ilimi da fahimta da hadin kai; wanda koyarwarsa ta wuce iyakoki kuma ya haɗa mutane tare.

“Rashin nasa zai kasance ga kowa da kowa, kuma abin da ya gadar zai karfafa mutane har abada.”

 

 

Daga Fatima Abubakar.