Babbar mota trailer ta murkushe wasu motoci hudu kusa da gadar Karu a kan babbar hanyar Abuja zuwa Nyanya Keffi a ranar Lahadi.Hatsarin ya haifar da cunkoson ababen hawa a kan hanyar.
Jami’an rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen Karu da na hukumar kiyaye hadurra ta tarayya sun isa wurin kusan nan take suka karkatar da ababen hawa zuwa titin ajiye motoci.
Da yake mayar da martani kan hatsarin, kwamandan sashin babban birnin tarayya, FRSC, Mista Samuel Ochi, ya bayyana cewa hatsarin ya faru ne da misalin karfe 9:30 na safe, amma ba a samu asarar rai ba.
A cewarsa, wadanda suka samu raunuka an garzaya da su asibiti domin yi musu magani.
“Kwamandan runduna ta FRSC da wasu jami’an mu suna wurin da hadarin ya afku. Sun tabbatar wa da wakilan mu cewa a gaskiya motar mu na kan hanyarta ta kwashe baraguzan da ke kan hanya amma babu wanda ya mutu.
Hukumar bada agajin gaggawa ta FRSC ta kwashe wadanda suka jikkata zuwa babban asibitin Asokoro dake Abuja domin yi musu magani.”
“Mun gode wa Allah ba a rasa rai,” in ji Attah.
wanda ya yi kira ga direbobin manyan motocin da su dinga gyaran motocinsu akan kari idan sun lura da abubuwan da ba daidai ba a yayin hawa ko sauka daga titin Abacha Barracks.
Attah ya kuma umarci direbobin manyan motoci da su rika tafiya a hankali yayin da suke saukowa daga bariki zuwa Kugbo, Karu da kuma Nyanya.
- Daga Fatima Abubakar