Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike ya warware takaddamar da ta shafe watanni ana yi dangane da kafa titin jirgi na biyu na filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja.
Majalisar zartarwa ta tarayya FEC a watan Maris 2022 ta amince da titin jirgi na biyu, inda aikin ya kasu kashi hudu. An kuma yi niyyar ƙaddamar da aikin a watan Yuni na 2023.
Sai dai wani bangare na al’ummar Jiwa da ke kan titin jirgin, sun nuna rashin amincewarsu da korarsu daga filayen kakanninsu, suna neman gwamnati ta biya su diyya.
A wani taron sasantawa da ’yan uwa da sauran masu ruwa da tsaki a ranar Talata, Wike ya ce ya fahimci radadin da suke ciki kuma zai yi iyakacin kokarinsa wajen ganin ba su hakkokinsu.
Don haka, ya ba da umarnin biyan diyyar Naira miliyan 825 ga masu filayen da abin ya shafa.
Da kuma ci gaba da aikin kashi na biyu da zarar an gama rattaba hannu kan takardun yarjejeniya.
Daga Fatima Abubakar.