Wasu ‘yan bindiga a ranar Juma’a sun kai hari kan ayarin motocin shugaban Omega Fire Ministries Worldwide, Apostle Johnson Suleman, a kan hanyar Benin zuwa Auchi, jihar Edo, inda suka kashe ‘yan sanda uku da wasu mutum hudu.
An tattaro cewa shugaban ya dawo ne daga wata tafiya da yayi inda ya nufi wata hanya a jihar a lokacin da ‘yan bindigar suka kai wa ayarin motocinsa hari.
Lauyan Suleman, Samuel Amune, wanda ya tabbatar da faruwar harin a yau Asabar ya ce malamin ya dawo ne daga wani shiri a Tanzaniya, inda ya kara da cewa ya tsallake rijiya da baya.
Ya ce, “Ya na dawowa daga tafiya sai wasu yan bindiga suka far masa. Uku daga cikin jami’an ‘yan sandansa, da sauransu, sun mutu. Yana komawa Auchi ne ‘yan bindigar suka kai masa hari tare kusa da Sabongida har zuwa bakin Warake da Auchi yana iyaka da Warake. Ya wuce Warake kuma yana shiga iyakokin Auchi lokacin da harin ya faru.”
Da yake mayar da martani kan lamarin a wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Juma’a, Suleman ya ce ya tsallake rijiya da baya, inda ya ce an kashe mutane bakwai a harin.
Ya ce, “An kai wa motata hari; sun budewa motata wuta suna ta fesa harsashi, matata da yarana suna cikin motar rakiya a gaba. Sun kashe ‘yan sanda; sun kashe sauran mutanen da ke kan daya motar rakiya da bas din da ke tare da mu. An kashe mutane bakwai da ke tafiya cikin ayarin motocin.
Da yake tsokaci kan lamarin, wani masani kan harkokin tsaro, Dickson Osajie, ya yi Allah wadai da rashin tsaro a jihar, musamman yadda harin ya faru da rana tsaka.
Ya ce, “Sun far masa (Suleman); An kashe mutane bakwai. Kasar ba ta da tsaro,ta yaya mutane za su yi yawo da bindigogi a kan babban titin kuma ba a gano su ba? Wannan lamari ne mai tashin hankali.”
Da aka tuntube shi dan jin martaninsa kan lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Chidi Nwabuzor, ya tabbatar da faruwar harin.
Ya ce an kashe mutane shida da suka hada da ‘yan sanda da direbobin Suleman, inda ya ce ana ci gaba da kokarin gano inda ma’aikaciyar gidan malamin ta ke.
Nwabuzor ya ce, “An tabbatar da harin. An yi shi da misalin karfe 5 na yamma a Auchi. Sun taso ne daga Benin, kan hanyar su da zuwa Auchi, sai aka kai musu mummunar hari, abin mamaki sai suka yi harbin kan motocinsu. An kashe ‘yan sanda uku; an kashe direbobinsa biyu; Wata ma’aikaciyar gida ce ta kashe kuma suna ci gaba da neman inda take. Yayin da muke magana, Apostle Johnson Suleman yana cikin koshin lafiya. An harbi daya daga cikin ‘yan bindigar, an kuma gano daya daga cikin motocin.
Daga Fatima Abubakar