Yayin da aka ci gaba da kai aikin agaji zuwa trademore da ke Lugbe, an samu asarar rai daya.

0
46

Ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka fara tun da sanyin safiyar Juma’a a Abuja, ya sake yin barna a babbar kasuwar hada-hadar kasuwanci da ambaliyar ruwa, inda aka yi asarar dukiyoyi na daruruwan miliyoyin naira.

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA ta bayyanawa manema labarai cewa direban Peugeot 406 mai lamba  YLA 681 FS ta nutse kuma har yanzu ba a ganta ba a titin Imo  Estate yayin da aka ceto wasu mutane 4 kuma suna cikin koshin lafiya.

An ga mazauna yankin a lokacin da aka yi ruwan sama, inda suke kokarin ceton rayukansu da kuma ceto dukiyoyinsu bayan da ambaliyar ruwa ta mamaye gidajensu.

Gidajen kasuwanci da yawa sun shafe tsawon shekaru suna fama da mummunar illa na ambaliya da rayuka da kadarori na biliyoyin Naira.

Mazauna wannan yankin sun ce suna zaune cikin kwanciyar hankali a duk lokacin damina,domin a 2022 ambaliya ba ta shafe su ba duk da yawan ruwan sama da aka samu a shekarar.

Godiya ga dabarun sake gyara injiniyan da mai gidan ya yi amfani da shi wanda ya tabbatar da fadada magudanar ruwa da rushe ginin da ke tsaye tare da filayen ambaliya.

Kamar yadda ya zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, masu ruwa da tsaki da suka mayar da martani ga ambaliyar sun hada da NEMA, Hukumar kashe gobara, FCT FEMA, Red Cross da ma’aikatar Muhalli-Flood na tarayya bi da bi.

Daga Fatima Abubakar.