ASUU TA KARA TSAWAITA YAJIN AIKI DA SATI TAKWAS.

0
68

Kungiyar Malaman Jami’o’i ta kara tsawaita yajin aikin da take yi da makwanni takwas bayan da Gwamnatin Tarayya ta gaza yin gamsasshen magance duk wasu batutuwan da aka tabo a yarjejeniyar aiki ta FGN/ASUU na shekarar 2020 a cikin yajin aikin gargadi na mako hudu.

Shugaban kungiyar, Emmanuel Osodeke ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Litinin.

Osodeke ya bayyana cewa Majalisar Zartaswar ta kasa a yayin taron ta a ranar Lahadi ta kammala cewa za su baiwa FG wa’adin makonni takwas don magance dukkan matsalolin “a zahiri” domin dalibai su dawo.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “NEC ta amince da kokarin shiga tsakani, ta hanyoyi daban-daban, da ’yan kishin kasa da abokan ci gaban kasa na gaskiya (dalibai, iyaye, ’yan jarida, shugabannin kungiyoyin kwadago, masu fafutukar kare hakkin jama’a da dai sauransu) suka yi don gaggauta magance rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa.

“Duk da haka, ASUU, a matsayin kungiyar masu hankali, tana da alhakin tarihi na sanya gwamnatoci su girmama yarjejeniyoyi.

By Fatima Abubakar