Yadda Ake hada doya da kwai (Yamarita)

0
1090

Doya da kwai wadda ake Kira da Yamarita da turanci abinci ne da kowa Ke so a Najeriya, sai dai inhar ba’a gwada ba.  Yamarita dafaffen doya ne da aka sa a cikin danyan kwai, flawa, citta, tafarnuwa, da gishiri, sai a soya.  Wannan shi ne daya daga cikin shahararrun abincin Hausawa.  ya kuma shahara kamar yadda suya watto balangu ya shahara.

Yamarita yana da saukin hadawa  kuma yana da dadi.  Kuna iya hada shi a cikin kusan mintuna 45 kawai.  Ana iya  hada yamarita da stew, miyan kwai, ko ketchup .

Abubuwan da ake bukata sune:

 

  • Doya- 1 kg
  • Kwai 3
  • Cokali 2 na flawa.
  • Man gyada (300ml).
  • Karamin Cokali na ginger.
  • Karamin Cokali na tafarnuwa.
  • 1 teaspoon na barkono.
  • 1 cube na knorr (mai zaki).
  • gishiri kadan

Wadannan sune Abubuwan da ake amfani da su wajen yin yamarita.

Yadda ake hada yamarita

  1. Da farko za’a fere bayan doyan, sai a yanka zuwa girma da sifan da ake so sai a dafa na kamar minti 15. Har sai Yayyi laushi kuma ya dahu sosai.  Sai a juye a matsama a barshi Yayyi sanyi.

  1. Sai a hada kayan kamshi duka ginger, tafarnuwa, barkono, Maggi, gishiri da kwai ukun da aka fasa. Sai a jujjuya yadda ya kamata.

 

  1. sannan sa a zuba doyan da aka dafa a ciki.

 

  1. Sai a daura kwanon suya akan wuta sai a zuba man gyada a ciki. Sai a barshi Yayyi zafi na kamar minti 1.

  1. A zuba dafaffen doyan a cikin hadin kwai ɗin sai a zuba a cikin mai mai zafi kuma a soya.

  1. Idan ba Soyu sai a juya dayan bangaren, kar a bari ya ƙone.

  1. Idan ya soyu sai a kwashe  aci tare da miyan  da mutum ya fi so ko Gasashen kifi ko kaji.

Daga: Firdausi Musa Dantsoho