2023: Kungiyar Yarbawa ta Arewa ta baiwa Tinubu tabbacin samun kuri’u miliyan 20

0
9

Gabanin zaben 2023, wata kungiya a karkashin kungiyar Yarbawa ta Arewa Agenda for Tinubu (NOYAT), ta tabbatar wa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC mai mulki, Bola Ahmed Tinubu kuri’u miliyan 20 tare da yin masa alkawarin ba shi goyon baya da tabbatar da burin cewa Tinubu ya zama shugaban kasa.

Kungiyar Arewa Yoruba ta ce suna da hanyoyin sadarwa a fadin jihohin Arewa 19 da suka hada da Babban Birnin Tarayya, kuma tuni aka samar da wani tsari na wayar da kan ‘yan kasa a kan dalilin da ya kamata Bola Ahmed Tinubu ya zama shugaban kasa na gaba a kasar nan a zaben 2023,” kungiyar

Da yake jawabi a wajen taron zaman lafiya da kuma addu’a ta musamman da aka shirya wa Bola Tinubu da kuma dan takarar gwamna na jam’iyyar APC na jihar Kaduna, Sen. Uba Sani a karshen mako a jihar Kaduna, kodinetan kungiyar na kasa Hon. AbdulRasheed Adekeye ya bayyana cewar goyon bayan da kungiyar ke baiwa Tinubu da Shettima ya samo asali ne daga irin nasarorin da suka samu.

A cewar kodinetan na kasa, matsayin NOYAT na goyon bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ya ta’allaka ne bisa ka’ida da akida ba bisa kabilanci ba.

“Mun kafa tantin mu tare da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu bisa gaskiya, adalci da kuma amana, kamar yadda gwamnonin APC suka nuna shi.”

Mun yi imani da iyawar Tinubu da Shettima, kuma hakan ya faru ne saboda abubuwan da suka bari a jihohin Legas da Borno a matsayin gwamnoni.

“Ba mu taba kasancewa cikin shakku kan iyawar Tinubu da Shettima na jagorantar kasar nan zuwa wani matsayi mai kishi wanda zai biya bukatun ‘yan Najeriya,” in ji Adekeyele.

Don haka ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su goyi bayan burin shugaban kasa na Tinubu, ya kara da cewa ‘yan Nijeriya kada su bari ‘yan siyasa masu son kai su yi amfani da su, wadanda ba su da wata manufa ta alheri ga kasa.

Haka kuma, a wajen taron, an gudanar da addu’a ta musamman a madadin Tinubu, Shettima da Uba Sani tare da fitattun malaman addinin Yarbawa na Arewa da masu rike da sarautar gargajiya da suka halarci wajen neman yardar Allah domin samun nasara. Yayin da aka kaddamar da CD na bidiyo da aka sadaukar don Tinubu.

Daga Faiza A.gabdo