Ministan Yada Labarai Ya Kafa Kwamitin Kare Hakkokin Nakasassu

0
14

Ministan Yada Labarai Ya Kafa Kwamitin Kare Hakkokin Nakasassu

 

Daga: Muhammad Suleiman Yobe

 

Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Mohammed Idris, ya ba da umarnin kafa wani kwamiti mai mutum biyar domin tsara aiki da hukumar nakasassu ta kasa domin wayar da kan jama’a game da ‘yancin nakasassu da kuma damar da suke da shi a rayuwa.

 

Mataimaki na musamman ga ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa

Rabiu Ibrahim ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai ciki harda jaridar DDL Hausa.

 

Ministan ya bayar da wannan umarnin ne a yau Laraba, a babban birnin tarayya Abuja lokacin da ya karbi bakuncin babban sakataren hukumar nakasassu ta ƙasa Dr. James Lalu a wata ziyarar ban girma da ya kai ofishin sa.

 

“Daga yau, za mu kafa kwamitin da zai yi aiki kafada da kafada da ku domin duba takamaiman bukatunku domin mu taimaka muku wajen ganin kun cimma su,” in ji Idris

 

Ministan ya ƙara da cewa Shugaba Tinubu ya yarda da shigo da jama’a cikin gwamnatinsa musamman wajen bawa nakasassu dama a gwamnatinsa.

 

Idris ya ƙara da cewa mutane miliyan 35 da ke fama da nakasa suna wakiltar wani muhimmin rukuni na al’umma wadanda ke da kwarewa, basira, da gogewa kuma za su iya daga kimar Nijeriya.

 

A nasa jawabin, babban sakataren hukumar nakasassu Dr. Lalu ya ce ya je ma’aikatar ne domin neman hadin gwiwa don wayar da kan nakasassu hakkinsu.

 

Dokta Lalu ya ce nakasassu na da baiwa da har kawo yanzu ba a iya amfani da ita ba a Nijeriya, wadanda suka hada da fasahohi daban-daban, cancantar kwarewa, da basirar da ake bukata don ci gaban tattalin arzikin kasa.

 

 

 

 

Hafsat Ibrahim