Gwamnan Gombe Ya Naɗa Muƙaddashin Shugaban Kwalejin Kimiyya Da Fasaha Ta Lafiya Dake Kaltungo

0
23

Gwamnan Gombe Ya Naɗa Muƙaddashin Shugaban Kwalejin Kimiyya Da Fasaha Ta Lafiya Dake Kaltung

Daga Yunusa Isah kumo

 

 

 

Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya, ya amince da naɗin Dakta Umar Mohammed a matsayin muƙaddashin shugaban riƙo na Kwalejin Kimiyya da Fasahar Lafiya ta Jihar Gombe dake Kaltungo.

Wata sanarwa da Babban Daraktan Yaɗa Labarun Gwamnan Jihar Ismaila Uba Misilli ya miƙawa Mujallar Tozali, ta ce Kwamishinan ilimi mai zurfi Mohammed Shattima Gadam ne ya sanar da amincewar Gwamnan, yana mai cewa naɗin na Dakta Umar ya biyo bayan murabus ɗin da tsohon muƙaddashin shugaban kwalejin Dr. Ahmed Wali Doho ya yi ne, kasancewar ya tsaya takaran shugaban Ƙaramar Hukumar Kwami a zaɓen ƙananan hukumomin da aka gudanar kwanan nan.

Dokta Umar Mohammed, kwararren malamin jami’a mai gogewa a fannin shugabanci da tattalin arziki, kafin naɗinsa ya kasance Daraktan Tsare-tsaren harkokin Ilimi na Jami’ar Tarayya ta Kashere.

Zai ci gaba da riƙe wannan muƙamin a matsayi na riƙon ƙwarya har sai an naɗa cikakken shugaba.

Gwamnan yana fatan sabon muƙaddashin shugaban zai yi amfani da ɗimbin ilimi da gogewarsa wajen gudanar da aikinsa don ci gaban kwalejin.

Naɗin ya fara aiki ne nan take.

 

 

 

Hafsat Ibrahim