Kotu ta gargadi jami’an tsaro da hukumar Hisbah tare da dakatar da su daga kama Mansura Isah

0
26

 

 

Babbar kotun tarayya karkashin jagorancin mai Shari’a Abdullahi Liman, ta takadar da hukumar Hisba da kwamishinan ƴan sanda da kuma mataimakin babban Sifeton ƴan sandan kasar nan daga kama Mansura Isa.

 

Mai Shari’a Liman ya ayyana cewar ya yi hani ga waɗanda akayi karar ko ƴan korensu ko wakilansu, ko kuma wasu masu aiki amadadinsu daga kamawa ko tsorataswa ko gayyata har zuwa lokacin da za’a saurari kowane ɓangaren.

Wannan umarni dai ya samu ne a cikin wata ƙara mai lamba 159/2024, wadda Mansura Isah ta shigar tana karar hukumar Hisba da kwamishinan ƴan sandan jihar Kano.

Kotun ta sanya ranar 15 ga wannan watan dan sauraron kowane bangare a shari’ar.

 

 

Hafsat Ibrahim