Shugaban kungiyar All okada Union Forum na karamar hukumar Gwagwalada da ke babban birnin tarayya Abuja, Malam Kabir Dahiru, ya roki gwamnatin tarayya da kada ta hana masu tuka babura a kasar nan, yana mai cewa galibin masu sana’ar babura sun kammala karatu.
Dahiru ya yi wannan roko ne a wata hira da manema labarai a lokacin babban taron kungiyar a Gwagwalada.
Ya kuma umarci gwamnati a dukkan matakai da su rika tafiya da masu babura a cikin shirye shiryensu.
Ya ce makasudin taron shi ne don wayar da kan masu tuka babura su kasance masu kula da harkokin tsaro a yayin gudanar da ayyukansu.
Daga nan sai ya shawarci masu tuka babura da su guji duk wani abu da zai iya bata musu suna a cikin al’umma, ya kuma gargade su da su kasance masu taka-tsan-tsan a koda yaushe.
Ya kuma yi nuni da cewa, shugabancinsa zai ci gaba da wayar da kan masu tuka babura a yankin, yayin da ya mika godiyarsa ga gwamnatin karamar hukumar Gwagwalada kan yadda suke tallafa wa masu tuka babura.
Shima da yake jawabi shugaban karamar hukumar Hon. Abubakar Jibrin Giri wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatan sa, Hon. Kasim Sani Mohammed ya ce hukumar gudanarwar karamar hukumar za ta samar da yanayi mai kyau ga masu tuka babura su yi aiki.
A martanin da suka mayar, jami’in ‘yan sanda mai kula da sashin Gwagwalada, CSP S.A Hamza wanda ya wakilta a wajen taron ya roki masu tuka babura da kada su dauki fasinjoji sama da biyu a kan baburansu.
wakilin NSCDC ya kuma bukaci masu babura da su kula da fasinjojin su.
Daga: Firdausi Musa Dantsoho