Tare da Muhammad Iskeel
ƙarshen watan Maris, an samu rahoton kisan gilla da akai wa wasu Hausawa yan arewa har mutane 16 a garin Uromi, cikin Karamar Hukumar Esan ta arewa, a jihar Edo.
Wannan mummunan aiki ya girgiza zukata, tare da haifar da damuwa da tsoro firgici da razani tsakanin al’ummar yankin da ma sauran ƙasa baki ɗaya.
A jihar Filato kuwa, hukumar bada agajin gaggawa ta ƙasa, NEMA, ta tabbatar da cewa wasu ‘yan bindiga sun kashe aƙalla mutane 52, tare da raba sama da mutuane dubu biyu da muhallansu, cikin hare-haren kwanaki da dama da suka faru a yankunan manoma da makiyaya.
Wannan kuwa wani sabon salo ne a cikin dadaddiyar rigimar da ke tsakanin manoma da makiyaya a wannan yanki.
A garin Otukpo ta Jihar Benue, har ila yau, an samu rahotannin kashe-kashe da garkuwa da mutane da ya dabaibaye yankin.
Amma fa zancen kisan gilla da satar bil-adama domin karbar kudin fansa ba a wadannan yankuna ya tsaya ba kadai,
domin akwai wasu jihohi da suka dade cikin wannan mummunan hali na rashin tsaro da kuma garkuwa da mutane.
A wasu sassan Jihar Kaduna, da jihar Katsina, da sassan jihar Zamfara, Sokoto, Kebbi da Niger, garkuwa da mutane ya zama ruwan dare, lamarin da har ya kai shekara fiye da goma, kuma a ainihin gaskiya, rahotannin da ake samu kan lamarin sun yi ƙasa da abin da ke ainihin faruwa.
Ma’ana dai, ana samun irin wadannan ta’annuti da dama amma babu mai ji.
Misali a karamar hukumar Ikara ta Jihar Kaduna, yan bindiga sun bi dare suka dauki wani bawan Allah, bayan sun tafi da shi sun bukaci kudi har Naira miliyan takwas, daga bisami bayan kai masu kudin sai dai tsintar gawan akai.
To ko me yasa wadannan matsaloli suka ki ci ballantana cinyewa?
To sanin gaibu sai dai Allah, amma dai komawa kacokan ga mahalicci babban dabara ce, musamman ganin dabarun mutune ya sami tazgaro.
Bayan addu a kuma masu ruwa da tsaki ya kamata su rubanya kokarinsu, domin Allah yana duba hobbasa da kokarin masu kokari.
Gwamnatin Tarayya ta kara kaimi, wajen daukar wannan lamari da muhimmanci matuƙa, ta hanyar tashi tsaye wajen kare rayuka da dukiyoyin ‘yan ƙasa.
Ya zama wajibi gwamnati ta ƙarfafa sojoji, ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro da kayan aiki da horo domin tunkarar ‘yan bindiga da suka addabi ƙasa.
Gwamnatocin Jihohi su ne ke kusa da al’umma, wajibi ne su jajirce, su inganta hanyoyin tsaro a cikin jihohinsu, ta hanyar amfani da hukumomin tsaro na cikin gida da kuma haɗin guiwa da shugabannin al’umma.
Shugabannin Addini da masu rike da sarautu su rika wayar da kan al’umma dangane da muhimmancin zaman lafiya da fahimtar juna.
Sannan su tsaya tsaka-tsaki, tare da amfani da matsayinsu wajen kawo fahimta tsakanin al’umma.
Hukumomin Tsaro su tashi tsaye wajen gudanar da bincike mai zurfi, su kamo wadanda ke da hannu cikin wannan kashe-kashe da garkuwa da mutane, tare da gurfanar da su gaban kotu domin hukunci mai tsanani.
Yan jarida da Hukumomin Yaɗa Labarai ya kamata su kara zage damtse, ba tare da nuna bangaranci ko jinsi ba, wajen fallasa gaskiya, da bayar da rahotanni na gaskiya da sa-ido kan gwamnati da hukumomin tsaro.
Al’umma gaba ɗaya lokaci ya yi da za mu daina ɓoye masu aikata laifi cikin mu. Dole ne mu kasance masu bayar da bayanai, tare da mara baya ga gwamnati da jami’an tsaro domin samun zaman lafiya.
Saura da me? Wajibi ne mu rika yabawa jami’an tsaronmu da basu kwarin gwiwa domin su kara kwazo.
Tsaro shi ne ginshikin cigaban al’umma a ƙasa. Ba za mu cigaba da zama cikin duhu, tsoro da zubar da jini ba, ba tare da ɗaukar mataki ba.
Dole ne mu tashi tsaye gaba ɗaya domin samar da zaman lafiya.
Najeriya tamu ce mu zamu gyara ta, ko mu ko akasin haka.
Publishing by Hafsat Ibrahim