Wike ya musanta rahotannin cewa Tinubu ya ba shi tikitin takarar Sanata

0
45

Mataimaki na musamman ga gwamna Nyesom Ezenwo Wike kan harkokin yada labarai, Kelvin Ebiri, ya musanta rahotannin da ke cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Sanata Ahmed Bola Tinubu, ya taba bai wa gwamnan jihar Ribas tikitin takarar Sanata.
Ebiri, a cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai kuma ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Asabar, ya bayyana labarin, wanda aka buga a jaridu da dama na kan layi a matsayin “karya, mara tushe kuma abin kunya.”

Sanarwar ta ci gaba da cewa: “An ja hankalinmu ga wani rahoto na batanci da wasu jaridun kasar nan da jaridun yanar gizo suka wallafa, musamman ma Sahara Reporters cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Ahmed Tinubu, ya ba wa gwamnan jihar Ribas, Nyesom. Ezenwo Wike, tikitin tsayawa takarar Sanatan APC.

“An zargi Gwamna Wike da bayyana hakan a yayin tattaunawar da aka yi a kafafen yada labarai da aka watsa a gidajen Talabijin na Channels, Television Independent Television, Nigerian Television Authority da TVC a ranar Juma’a, 23 ga Satumba, 2022.

“Muna so mu bayyana a fili cewa wannan labarin karya ne, marasa tushe domin gwamnan jihar Ribas a duk tsawon hirar da ya yi da manema labarai bai ambaci sunan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ba ko kuma ya yi nuni da cewa ya ba shi tikitin takarar Sanata.

“Don bayyana gaskiyar lamarin, mun yanke shawarar shigar da bayanan abin da gwamna Wike ya fada dangane da fom din Sanata.

Gaga Faiza A.gabdo