Jama’a Sun Yi Gangami a Jahar Zamfara Domin Tarbar Dan Takarar Gwamnan a karkashin Jam’iyyar PDP DR.Dauda Lawal Bayan da Kotu ta maida shi .

0
83

Kotun Daukaka Kara Ta Dawo Da Dauda Lawal A Matsayin Dan Takarar Gwamnan Jihar Zamfara A PDP

Dr  Lawal ya ce hukuncin na daukacin al’ummar jihar ne ba jam’iyyar kadai ba.

Kotun daukaka kara da ke Sokoto ta mayar da Dauda Lawal a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Zamfara .

A baya wata babbar kotu da ke zamanta a Gusau a jihar Zamfara ta soke zaben fidda gwanin da ya gabatar da Mista Lawal.

Alkalin kotun, Aminu Bappa – Aliyu, ya ce jam’iyyar PDP ba ta da dan takarar gwamna a jihar.

A hukuncin da ta yanke, kotun daukaka kara a ranar Juma’a ta yi watsi da hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke.

A hukuncin da Muhammad Shuaibu da wasu mambobin kwamitin guda biyu, kotun ta umurci hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da ta amince da Lawal a matsayin zababben dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Zamfara a zaben 2023 mai zuwa.

Da yake mayar da martani kan hukuncin, Dauda Lawal, a wata sanarwa da ofishin yada labaransa ya fitar, ya bayyana hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke a Sokoto “a matsayin nasara ga dimokradiyya, mutanen jihar Zamfara.

“Hukuncin kotun daukaka kara nasara ce ba ga jam’iyyar PDP kadai ba amma ga daukacin al’ummar Zamfara masu kishin shugabanci na gari.

Daga Fatima Abubakar.