Tsoffin ma’aikatan Twitter da ke Ghana sun ce kamfanin ya yi shiru kan duk wata tattaunawa da lauyoyinsu bayan da aka kore su daga aiki a watan Nuwamban bara.
Sun kuma ce ba a biya su kudaden sallamar su ba.
Agency Seven Seven, dake wakiltar tsofaffin ma’aikatan da suka fusata, ta ce Twitter bai tuntubi su ko ma’aikatan ba tun watan Mayu lokacin da aka kusa kammala tattaunawa.
Hukumar ta ce katafaren dandalin sada zumunta, ta hannun kungiyar lauyoyinta, ya kusa cimma yarjejeniya kan biyan ma’aikatan da aka kora albashin watanni uku da kuma kudaden mayar da wadanda aka dauka daga wajen Ghana, amma shiru ta yi na tsawon makonni.
Hukumar Agency Seven Seven ta ce yanzu tana binciken wasu hanyoyin da za a bi. Ana fargabar cewa rashin sasantawa na iya haifar da mummunan misali ga yadda kamfanonin ketare ke daukar ma’aikata a Ghana.
Kamfanin Twitter ya bude ofishinsa na Afirka daya tilo a Ghana a watan Nuwamban da ya gabata kuma yana da ma’aikata kusan goma sha biyu amma sai aka sallame su daga aiki a matsayin wani bangare na tsarin ma’aikatan duniya da Elon Musk ya bullo da shi lokacin da ya sayi kamfanin.
Har yanzu Twitter bai amsa bukatar BBC na yin sharhi ba.
Firdausi Musa Dantsoho