Yan Kasuwar Mai Sun Daidaita Fafunarsu Yayyin Da Farashin Man Fetur Ya Kai N617/Lita

0
16

An daga farashin famfon na Premium Motor Spirit, wanda aka fi sani da man fetur daga N537/litta zuwa Naira 617/lita a wasu gidajen mai da Kamfanin Man Fetur na Najeriya NNPC da ke Abuja ranar Talata.

‘Yan kasuwar mai masu zaman kansu sun tabbatar da karin farashin kayayyakin, domin sun bayyana cewa duk wani sauyi na farashin da gidajen man na NNPC ke yi alama ce ta tashin farashin mai.

“Hakan ya faru ne saboda har yanzu NNPCPL ce ke kan gaba wajen shigo da man fetur a Najeriya a halin yanzu, duk da cewa sauran ‘yan kasuwa na shigo da kayan a hankali. Farashin da safiyar yau (Talata) a wasu gidajen man NNPC ya kai N617/Lita,” Sakataren kungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta ta Najeriya Abuja-Suleja Mohammed Shuaibu, ya shaida hakan.

Idan dai za a iya tunawa, Shugaba Bola Tinubu ya yi jawabin bude taron a ranar 29 ga watan Mayu, inda ya bayyana cewa tallafin man fetur ya kare, lamarin da ya janyo tashin farashin mai daga N198/litta zuwa sama da N500/lita a ranar 30 ga watan Mayun 2023.

Tun bayan janye tallafin man fetur da kuma saukan darajan Naira akan dala, ‘yan kasuwa sun ci gaba da bayyana cewa farashin mai zai iya tashi har N700/litta.

Hakazalika, hauhawar farashin danyen mai a kasuwannin duniya shi ma ya kara haifar da tashin gwauron zabin man fetur, kasancewar danyen shi ne samfurin da ake samar da mai da sauran kayayyakin da aka tace daga gare su.

A Abuja, a safiyar ranar Talata, masu ababen hawa sun cika gidajen man da har yanzu ake ci gaba da sayar da man fetur a kan Naira 540, amma da labarin karin farashin da tashoshin NNPCPL suka yi, ya sa da yawa daga cikin gidajen mai masu zaman kansu suka kulle tashoshinsu.

Wasu kuma nan da nan suka fara gyaran famfunan nasu don nuna sabon farashin. Har yanzu dai hukumar ta NNPC da mai kula da bangaren mai ba su yi wani bayani kan ci gaban da aka samu ba.

Firdausi Musa Dantsoho