Yadda zamu yi haddin tafarnuwa da citta(Ginger & Garlic paste)

0
468

Hadin tafarnuwa da citta watto ginger and garlic paste hadi ne da keda amfani sosai wajan girki, wasu na amfani da waenan sinadaran kamshi da dandano a kowani girkin su.

Wanan hadin na iya yiwa mutun wata daya ba tare da ya bace ba, kuma yana kawo saukin bare tafarnuwa da citta a kullum.

ABUBUWAN BUKATA SUNE:

  • Tafarnuwa kofi biyu
  • Citta kofi daya
  • Man gyada cokali shida

YADDA AKE HADAWA

  1. Zamu bare tafarnuwan mu da citta.
  2. Mu yanka tafarnuwan mu da citta kanana.
  3. Sai mu zuba su a cikin blender inmu da man gyadan mu, sai mu nikka yayyi laushi.
  4. Idan yayyi laushi toh hadin tafarnuwan mu da citta yayyi.
  5. Mu samu kwalba mai murfi mu zuba a ciki mu sa a cikin fridge .

ABUN LURA: zamu iya anfani da wanan hadin a dafa dukan shinkafa, tafasan naman mu, miyan kuka da ma abinci da yawa domin kara masa daddi da dandano.

Rubutawa:Firdausi Musa Dantsoho