Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana kaduwarsa dangane da juyin mulkin da ya hambarar da gwamnatin Mohammed Bazoum na jamhuriyar Nijar.
Tsohon shugaban kasar, ya ce ya ji dadin yadda shugaban kasa Bola Tinubu ya fara tunkarar wannan ci gaba.
Buhari ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Twitter ranar Juma’a.
Tsohon shugaban na Najeriya ya ce yana da kwarin gwiwa kan yadda Shugaba Tinubu zai iya magance rikicin.
Buhari ya tabbatar wa da jama’a cewa Tinubu zai iya sauya lamarin da kuma tabbatar da tsaron Bazoum da iyalansa.
“Kamar yadda ake tsammani, ni, kamar sauran miliyoyin ‘yan Nijeriya, na yi mamakin sabon al’amura a jamhuriyar Nijar.
“An nuna damuwa game da makomar dimokuradiyya a matsayin tsarin gwamnati a kasar nan da ma sauran yankuna, haka ma, game da lafiyar Shugaba Mohammed Bazoum da iyalansa.
“Ni da iyalina mun damu da waɗannan kamar kowa.
“Abin farin ciki ne ganin cewa kungiyar ECOWAS, karkashin jagorancin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ta rigaya ta shawo kan lamarin yadda ya kamata.
“Kuma fatanmu da addu’o’inmu shine cewa yanayin da ba a so ya koma gaba daya, kuma an tabbatar da amincin shugaba Bazoum da danginsa.”
Daga Abubakar Abubakar.