Ba za mu iya tabbatar ko musanta zargin kama mataimakiyar gwamnan CBN, Aisha Ahmad – DSS ba

0
45

 

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta bayyana cewa ba za ta iya tabbatarwa ko karyata kame mataimakiyar gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) mai kula da harkokin kudi, Aisha Ahmad ba.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa hukumar DSS ta kama Ahmad da safiyar ranar Lahadi.

Wata majiya a rundunar ‘yan sandan sirri ta shaidawa News Point Nigeria cewa, ana yi wa mataimakiyar gwamnan babban bankin CBN tambayoyi kan yadda bankin Titan Bank ya tara dala miliyan 300 don kammala sayan bankin Union.

A cewar majiyar, sashen ya kuma kwace kayan lantarki na Ahmad tare da kwashe wasu takardu daga gidanta da ofishinta.

Da aka tuntubi mai magana da yawun DSS, Peter Afunanya, a ranar Lahadi, ya shaida wa News Point Nigeria cewa ba za su iya tabbatarwa ko musanta cewa Aisha na hannunsu ba ko kuma an gayyace ta domin amsa tambayoyi.

Ya bayyana cewa a duk wani bincike, ana iya gayyato mutane domin yin musu tambayoyi sannan kuma ana gudanar da wannan gayyata ne bisa tsarin doka.

Wannan na zuwa ne kimanin watanni biyu bayan da hukumar sirri ta kama tsohon shugaban Aisha a babban bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele. Tun a lokacin yana hannun DSS.

Da farko dai an tuhumi Emefiele, gwamnan babban bankin Najeriya da aka dakatar da laifin mallakar makami amma daga baya aka tuhumi shi da laifin almundahanar Naira biliyan 6.9.

Firdausi Musa Dantsoho